An samu rudani a unguwar Alwaza da ke karamar hukumar Doma a Jihar Nasarawa, yayin da aka yi garkuwa da yara ‘yan makaranta akalla shida a makarantar firamare a ranar Juma’a.
Hakan dai na zuwa ne kamar yadda rundunar ‘yansandan jihar, ta ce an sace dalibai biyu ne kawai a kan hanyarsu ta zuwa makaranta, ba dalibai shida ba.
- Dimokuradiyya Ta Zauna Daram A Nijeriya, Ba Batun Juyin Mulki – Shugaban Tsaro
- 2023: Manyan ‘Yan Takara Na Shafa Wa Juna Kashin Kaji
Wata majiya a unguwar da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:00 na safe a lokacin da sauran daliban makarantar ke ci gaba da zuwa.
Ya ce, “Ba mu taba tsammanin faruwar irin wannan abu a cikin al’ummarmu ba.
“Yaran ‘yan makarantar, kimanin shida daga cikinsu, ‘yan bindiga dauke da muggan makamai ne suka yi garkuwa da su, inda suka tafi da su inda ba a sani ba.
“A matsayinmu na mazauna unguwar, ba za mu iya yin wani abu don kubutar da su ba, saboda masu laifin suna da makamai amma mun sanar da ‘yansanda halin da ake ciki kuma na yi imanin cewa za su yi kokarin kubutar da daliban da aka sace.”
A halin da ake ciki, kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya karyata ikirarin cewa an yi garkuwa da wasu daliban makarantar firamaren na, Alwaza, a harabar makarantar.
Ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun sace dalibai biyu ne kawai.
Ya ce sun hada da yara maza biyu ‘yan shekara bakwai zuwa takwas, inda suka kara da cewa suna kan hanyarsu ta zuwa makaranta ne lokacin da lamarin ya faru.
Sai dai kakakin, ya ce ‘yansanda suna samu labarin, kwamishinan ‘yansandan, Maiyaki Baba, ya jagoranci jami’an rundunar, da kungiyoyin ‘yan banga da sauran jami’an tsaro zuwa wurin da harin ya faru.
Ya ce, “Bayanan da nake samu sun ce an dauke yaran maza biyu masu shekaru daga tsakanin bakwai zuwa takwas a hanyarsu ta zuwa makaranta a makarantar firamare ta kauyen Alwaza.
“Da samun bayanan da misalin karfe 7:10 na safiyar yau, tawagar hadin guiwa karkashin jagorancin kwamishinan ‘yansanda da suka hada da ‘yansanda, sojoji da ‘yan banga suka tattaru zuwa wurin da harin ya faru domin kubutar da daliban da aka yi garkuwa da su tare da bankado wadanda wuka aikata laifin.
“Har yanzu muna kokarin gano ‘yan bindigar kuma mun yi alkawarin yin duk abin da za mu iya don magance lamarin.”
Ya yi kira ga mazauna yankin Alwaza da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu ba tare da wata fargaba ba.
Kakakin ya yi kira da su kai rahoton duk wata fuska da ba a saba gani ba a yankin ba ga ofishin ‘yansanda mafi kusa da su.