’Yan Boko Haram Sun Sake Kwace Damasak A Jihar Borno

Sun Harbo Jirgin Majalisar Dinkin Duniya

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

Rahotanni daga Jihar Borno a Arewacin Nijeriya sun bayyana cewa, kungiyar ’yan ta’addan Boko Haram ta sake kwace Damasak, shalkwatar karamar hukumar Mobbar, dake Jihar Borno, bayan ba-ta-kashin da suka yi da jami’an tsaron Nijeriya a yankin.
Bugu da kari, garin Damasak yana kan iyaka da Jamhuriyar Nijar ne, kana mai tazarar kilomita 160 daga arewacin babban birnin jihar ta Borno, wato Maiduguri, wanda kuma yanki ne da ya sha faman hare-haren mayakan Boko Haram.
A bangare guda kuma, wasu bayanan da ba a tantance sahihancinsu ba, sun nuna cewa, maharan sun harbo wani jirgi mai saukar ungulu na Majalisar dinkin Duniya a yankin.
Har wala yau, wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun kai wannan farmaki ne a garin Damasak tun a yammacin ranar Lahadi ta hanyar amfani da motoci makare da abubuwa masu fashewa hadi da makaman roka da su ka rinka cilla wa sansanin sojojin Nijeriya da ke garin, al’amarin da ya tilasta wa daruruwan jama’ar garin shiga daji don ceton rayukansu.
Dadin-dadawa, wata majiyar ta nuna cewa sojojin Nijeriya sun kashe yan ta’addan da dama, a hannu guda kuma, wasu jami’an tsaro tare da jama’ar garin sun mutu a harin yayin da karin wasu kuma su ka yi batan-dabo a wannan hari na Damasak.
A hannu guda, wata majiyar jami’an tsaro a yankin ta bayyana cewa, “Bayanai sun bayyana cewa Boko Haram sun mamaye garin Damasak bayan sun kwace shi a wani harin da su ka kai wa sansanin soji da ke garin.
“Haka kuma, akwai karin wasu bayanan sun maharan sun kwarari cibiyar kula da ayyukan jinkai ta Majalisar dinkin Duniya (UN) a tsammanin sojoji sansanin sojoji ne. Kuma akwai yuwar harin ya shafi jirgi mai saukar ungulu da suke amfani da shi.”
Haka zalika, idan za a tuna, ko a faifan bidiyon da shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fitar kwanan nan, ya yi barazanar kai hare-hare.
A karshe duk kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar yan-sanda a jihar, DSP Edet Okon domin samun tabbacin kai harin, abin ya ci tura.

Exit mobile version