Dalibai wadanda ya kammala aji 3 na babbar makarantar Sakandare a Brilliant Footsteps International Academy, Sokoto sun kera mota mai amfani da lantarki, wadda a makarantar suka fara yin abin tun da farko.
Irin wannan ci gaban da aka samu daga makarantun da ke Arewacin Nijeriya ba karamin ci gaba bane,aka samu ta tafarkin ilimin wanda abin burgewar abin tamkar daga bangaren ilimin Sakandare babba.
- Ba Tsoro Ne Yasa Muka Amince Da Sulhu Da Ƴan Bindiga Ba – Gwamnatin Sokoto
- 2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC
Mota mai amfani da lantarki mai sunan BMT 1.0, ‘yan makaranata ne wadanda suka kammala karatun babbar Sakandare a matsayin wani aikin da aka basu dake nuna lalle sun koyi wani abu a makarantar.
Namijin aikin da daliban suka yi wani abu ne da ke nuna cewar ko shakka babu,an samu babban ci gaba ta bangaren ilimin fasaha,tayadda su fa,dalibai, ne da suka kammala aji 3,na babbar Sakandare ba wata Kwalejin fasaha ko Jami’ar fasaha suka je,ba,nayadda suka kera mota mai amfani da lantarki wato da ake kira da suna BM1.0.
Daliban dai sun samu kulawa ce da kuma shawarwari daga Maglush Electrical Company, kamfanin da ya kasance wanda kebasu kulawa ta musamman dangane da hakan.
Da yake kaddamar da motar,mai makarantar wanda kuma shi ne Shugaba ko babban manaja, Dakta Shadi Sabeh,ya jinjinawa daliban kan namijin aikin da suka yi na fannin fasaha.
Kamar yadda yace, “wannan ba aikin da makaranta ta bada kawai bane,amma wani sako ne,da yake nuna matukar aka bada taimako,da kulawar da ta kamata, matasanmu ba karamin ci gaba za su kawo ma nahiyar Afirka ba.”
Motar BMT 1.0 tana amfani ne da kulawar Batiri (BMS), wanda yake bukatar a caza shi daga awa 3 zuwa 4,za kuma a iya tafiyar kilomita 30 matukar har ya samu cajin daya dace.Yana amfani abubuwa 3 na launin injiniya:da suka hada da (wani aiki na kanikanci),(shirya wayoyin lantarki)da kuma (yadda jikin zai kasance).
Shugaban tawagar Ahmed Shadi,ya bayyana cewa dalibai, “15 suka hadu kowane dga cikinsu da akwai irin gudunmawar daya bayar ta yadda hakar tasu ,ta samu cimma ruwa.Kowa ya bada bada irin ta shi basirar ta fasaha data kunshi yadda za a sa wayoyi, chassis fabrication zuwa yadda za a raba wuta da kuma gwada fasahar zamani.”
Daya daga ciukin wanda ya fi bada gudunmawa dangane ta tafiyar,Aisha Ahmed,ta yi bayai kan muhimmanci aikin da aka yi. “Idan har aka ci gaba da inganta lamarin, hakan zai rage yawan kudin safarin da ake biya,rage lalata muhalli, da kuma taimakawa Nijeriya yadda za ta bar shigo da motoci daga kasashen waje, kamar yadda ta bayyana”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp