’Yan Nijeriya 2,114 Aka Dawo Da Su Daga Libiya –NAPTIP

Daga Umar A Hunkuyi

Hukumar hana fataucin mutane ta kasa NAPTIP, ta ce ya zuwa yanzun an sami nasarar ceto sama da ‘Yan Nijeriya 2,114, ta hanyar kwaso su daga kasar Libya.

Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar, Mista Josiah Emerole, ne ya bayyana hakan ranar Asabar a Abuja.

Emerole, wanda ya hakaito babban daraktan hukumar, Malama Julie Donli, tana wannan bayanin a lokacin da take jawabi wajen taron bikin cika shekaru 60 na hamshakin dan kasuwan nan Kaftain Idahosa Okunbo, a Jami’ar Benin.

Okah-Donli, ta kirayi al’umma da kungiyoyi da su agazawa wadanda aka dawo da su din, ta yanda za su ji cewa yanzun sun iso gida wajen gudanar da lamurran rayuwarsu.

Shugabar Hukumar ta NAPTIP, har ila yau ta ja kunnen Matasan Nijeriya da su daina kwadayin barin kasan nan zuwa kasashen waje da nufin neman abin duniya.

Tana mai cewa, mamugunta suna nan boye a dukkanin sassan kasan nan, wadanda suke rudin matasa da sunan za su kai su wajen kasarnan, amma daga bisani, matasan ne suke bautarwa su kuma su cika aljihunansu. Okah-Donli, ta kuma bayar da shawarar a kara bude hanyoyin kasuwanci da kuma zuba jari da kasashen waje domin habaka tattallin arzikin Nijeriya.

“Ya kuma wajaba, gwamnati ta samarwa da matasa ayyukan yi, ta yanda hakan zai baiwa matasan karfin gwiwar zama a cikin kasar haihuwar su, ya hana su kwadayin barin kasar nan, zuwa wajen domin neman abin duniyan,” in ji Okah-Donli.

 

Exit mobile version