Connect with us

TATTALIN ARZIKI

‘Yan Nijeriya Da Dama Za Su Talauce Bayan Korona – Esele

Published

on

Tsohon shugaban kungiyar sufuri (TUC), Kwamared Peter Esele, ya bayyana cewa, ‘yan Nijeriya da dama za su talauce bayan wucewar cutar Korona, domin kananan kasuwanci da kuma kamfanoni za su durkushe. Haka ma jam’iyyar YPP ta bayyana hakan lokacin da ta ke korafi idan gwamnatin tarayya ba ta inganta harkokin lafiya da na fannin ilimi ba, to za a ci gaba da samun kangin talauci a Nijeriya. Esele da kuma jam’iyyar YPP sun bayyana hakan ne lokacin da suke mayar da martini a kan rahoton da Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) wanda ta fitar a jiya, inda take nuna cewa, a yanzu ‘yan Nijeriya sun kai miliyan 82.9 da ke fama da talauci, wanda ta nuna cewa akwai bukatar ballo da wani tsari wanda zai bunkasa kananan kasuwanci domin tsomo miliyoyin mutane daga kangin talauci.

Esele ya kuma taba rike mukamin shugaban kungiyar masu jigilar albarkatun mai da kuma gas ta Nijeriya (PENGASSAN), ya zargi gwamnatin tarayya da karuwar talauci a cikin wannan kasa, saboda rashin gyara wutar lantarki a Nijeriya.

Ya ce, “ban tunanin gwamnati ta yi wani kokari na a zo a gani a cikin wannan lamari. Ba wai a cikin wannan gwamnatin da take garagar mulki a yanzu ba, lamarin ya dade yana faruwa. A ko da yaushe muna bayar da shawarwari a kan a samo mafita a yadda talauci ke kara tatutu a Nijeriya.

“Ba mu da kyakkyawan tsari a cikin kasar nan kamar yadda kasar China ke yi. Ya kamata mu gudanar da tsari na shekara 10 wanda zai cire mutane miliyan 50 daga kangin talauci a cikin kasar nan. Idan muna so hakan ya tabbata akwai hanyoyin da ya kamata mu bi, ba wai ta hanyar bayar da kyaututtukan kudi ba ne lamarin zai kasance, saboda idan ana bayar da kyautar kudade, to zai kara haifar da wani talaucin. Ya kamata a yi amfani da hanyar da ta dace ta yadda kowa zai iya tsayuwa da kafafuwarsa.

“A Duniya baki daya, Nijeriya ce mai yawan sababbin kamfanonin na gwamnati masu bunkasa tattalin arziki, amma gwamnati ta kasa gyara wannan nan kamfanoni, ya kamata ta samo hanyoyin gyara wadannan kamfanoni domin bunkasa tattalin arziki.

“Farkon abin da na ke so gwamnati da yi shi ne, ta yi wa dukkan kamfanonin nan rijista tare da sanin yawansu, ta hanyar jhaka ne za a samu dinbin aikin yi a cikin kasar nan. Ana bayyanar da wadannan kamfanoni ta hanyar musu rijesta, to za a kowo kan matsalar rashin aikin yi a cikin kasar nan.

“Maganar gaskiya ita ce, lokacin da hukumar NBS ta fitar da wannan adadi, ba ta hada da lokacin da ake fama da annobar cutar Korona ba. Bayan wucewar cutar Korona, za a samu durkushewar kananan masana’antu. Ba mu da wani tsari da zai farfado da wadannan kasanan masana’antu, domin su samar da ayyukan yi. Idan mu na da tsarin da zai farfado da kananan masana’antun, to za mu iya rage yawan talauci a cikin wannan kasa.

“Haka kuma rashin wutar lantarki Nijeriya ya kara haddasa talauci. Mun kai shekara 20 mu na gudanar da mulkin dimokradiyya. Wannan lamari ya isa a ce mun gyara matsalolin wutar lantarki a cikin kasar nan. Idan aka magance matsalolin wutar lantarki, za a magance matsalar wutar lantarki wanda kamfanoni ke mafa da shi. Dukkan kudaden da gwamnatin ke rabawa ba za su taimaka ba. Ya kamata gwamnati ta yi amfani da wannan kuli wajen farfado da tattalin arziki wanda zai samar da ayyukan yi a cikin kasar nan,” in ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: