‘Yan Sanda Sun Bankado Kamfanin Sayar Da Jarirai A Legas

‘Yan Sanda a birnin Legas da ke sun sanar da kubutar da wasu ‘yan mata goma sha tara dauke da ciki a wani gida da ake sayar da jarirai da ke Unguwar Ikotun, inda suka kama mutum biyu da ake zargin suna da hannu wajen ajiye su.

Mai Magana da yawun rundunar, Bala Elkana ya shaidawa manema labarai cewar DPO da ke kula da Ofishin ‘yan Sandan Isheri-Osun, Chike Ibe ne ya jagoranci aikin bankado gidan, inda aka samu ‘yan matan dauke da juna biyu.

Sanarwar ‘yan Sandan ta ce ‘yan matan da suka fito daga Jihohin Ribas da Kuros Ribas da Akwa Ibom da Anambra da Abiya da kuma Imo sun yi zargin cewar an kama su ne a yi musu fyade, kuma idan sun samu ciki, sai a tsare su har sai sun haihu domin a sayar da jariran.

Rundunar ‘yan Sandan ta ce yanzu haka tana tsare da Happiness Ukwuoma da Sharifat Ipeya da ake zargin suna kula da gidan, yayin da shugabar su Madam Oluchi ta yi batar dabo.

Exit mobile version