Rundunar ‘yan sandan kasar Birtaniya ta kama tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, da matarsa, Misis Beatrice Nwanneka Ekweremadu, kan zargin hada baki da shirya kai wani yaro Birtaniya domin amfani da sassan jikinsa.
Ekweremadu, mai shekaru 60, da Beatrice, mai shekaru 55, ‘yan Nijeriya ne da aka tsare su a gidan yari kuma za su gurfana a gaban Kotun Majistare ta Uxbridge a ranar Alhamis.
An tuhume su da laifin hada baki don shirya tafiya da wani yaro da nufin yin amfani da sassan jikinsa a kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp