Babban zaben shugaban kasar Amurka da ake gudana yanzu na hargitsewa sosai, saboda ganin ’yan siyasar kasar na cire marufin bakin da su kan sanya na bayyana mutunci da nagatattun halaye, har ma suna daukar tsattsauran ra’ayi, ciki hadda ra’ayi na kyamar kwararru da fitattun mutane, amma sun yi biris da tushen muradun jama’a.
Mai kudi Elon Reeve Musk, ya zuba kudade da dama don goyon bayan Donald Trump, da zummar kawo tasiri ga sakamakon zabe. A wani bangare na daban, jam’iyyar Demokuradiyya sun yi amfani da Jimmy Carter, tsohon shugaban kasar mai shekaru fiye da dari a duniya don neman karin goyon baya. Wannan zabe babu ruwan nagartattun manufofin da ’yan takara za su dauka bayan sun ja ragamar mulki da karfin takara, sai ya zama takara ce a bangaren kudade da iko, wannan abin kunya ne.
- Yau Amurkawa Ke Kaɗa Ƙuri’ar Zaɓen Shugaban Ƙasa
- Dole Ne A Gyara Kuskuren Da Tsirarrun Kasashe Suka Yi Na Kiyaye “Dangantakar Diflomasiyya” Tsakaninsu Da Yankin Taiwan
Cibiyar nazari ta Pew ta kasar Amurka ta jin ra’ayin jama’a a watan Satumban bana cewa, tabbacin jiyya batun da ya kai matsayi biyu a cikin abubuwan da suka fi jawo hankulan masu kada kuri’u ban da batun raya tattalin arziki. Amma, a zaben na wannan karo, jam’iyyun biyu da kyar suke mai da hankali kan wannan muhimmin batu. Sun mai da samun kuri’u a gaban komai, yayin da muradun jama’a ya koma karshe. Ban da wannan kuma, Jama’ar kasar da dama na ganin cewa, akwai bambancin ra’ayi mai tsanani a wannan karo. Kamfanin dillancin labarai na AP, da cibiyar nazarin harkokin jama’a ta Amurka sun saurari jama’a a kwanan baya, wanda ya nuna cewa, da yawan masu kada kuri’u da suka yi rajista da yawansu ya kai kaso 40%, sun nuna matukar damuwa kan bullowar matakan nuna karfin tuwo bayan zaben, saboda rashin amincewa da sakamakon wannan babban zabe.
Fito-na-fito mai tsanani tsakanin jam’iyyun biyu, abubuwan kunya da ’yan siyasa suke yi, sun jefa jama’a musamman ma al’ummar Amurka cikin shakku. Zaben da ake fatan a bayyana demokuradiyya da adalci a cikinsa, alal hakika masu kada kuri’u suna iya zabi Trump ko Harris wadanda suke wakiltar moriyar jami’yyunsu kawai. Ina demokuradiyya? Yaushe za a kawo karshen wannan wasan kwaikwayo na rashin kunya? Ta yaya za a iya mai da hankali, da kuma tabbatar da muradun jama’a? (Mai zane da rubutu: MINA)