Abba Ibrahim Wada" />

‘Yan Wasan Senegal Sun yi Kokari — Mane

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta kasar Senegal, Sadio Mane, ya bayyana cewa tawagar ‘yan wasan kasar sunyi kokari bayan da suka buga wasa canjaras, 1-1 da tawagar ‘yan wasan kasar Brazil a ranar Alhmis.

Tawagar kwallon kafa ta Brazil ta tashi 1-1 da ta Senegal a wasan sada zumunta da suka yi ranar Alhamis a Singapore kuma dan wasan Liberpool, Roberto Firminho ne ya fara ci wa Brazil kwallo, bayan da Gabriel Jesus ya ba shi kwallon.

Ita kuwa Senegal ta farke ne ta hannun Famara Diedhiou a bugun fenariti, bayan da aka yi wa Sadio Mane keta a da’ira ta 18 wanda hakan yabawa kasar ta Sebegal samun maki daya akan zakarun na duniya.

A karawar ce Neymar ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Brazil wasa na 100, kuma an ba shi riga mai lamba 100 tun kan fara fafatawar sannan sau biyu Neymar ya kusan cin kwallo a bugun tazara, inda ta farko ta fada saman raga ta biyu kuwa mai tsaron raga Alfred Gomis ne ya ture ta.

Ita ma Senegal ta kai hare-hare da dama musamman wadda dan wasan Liberpool, Sadio Mane ya buga kwallo ya bugi turke yanzu kuma Brazil za ta buga wani wasan sada zumunta da tawagar kwallon kafar Najeria ranar 13 ga watan Oktoba a dai birnin na Singapore.

Wannan ne karo na biyu da tawagogin biyu za su fafatawa, tun bayan shekara ta 2003 inda Brazil ta yi nasara da ci 3-0 a Abuja idan dai ba’a manta ba Brazil ce ta lashe gasar cin kofin Copa America da ta karbi bakuncin wasannin, ita kuwa Najeriya ce ta yi ta uku a gasar kofin nahiyar Afirka da aka yi a kasar Masar.

Exit mobile version