Yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, ya sake zama wuri mafi ’yancin hada-hadar tattalin arziki a duniya, kamar dai yadda wani rahoton bincike ya tabbatar.
Rahoton na shekara-shekara, wanda cibiyar “Fraser” ta fitar a jiya Talata, wanda ya fayyace yanayin ’yancin hada-hadar tattalin arzikin duniya na shekarar 2026, ya bayyana sassa biyar da binciken ya mayar da hankali a kansu, inda yankin HK ya wanzar da fifikonsa a matakin farko a fannin “’yancin yin cinikayya tsakanin kasa da kasa”, kana da matsayi na biyu a fannin aiwatar da “dokoki.”
Wani kakakin gwamnatin yankin na HK, ya ce rahoton ya sake jaddada karfin ikon yankin, a matsayinsa na dandalin hada-hadar tattalin arziki mai ’yancin gudanar da kasuwanci, wanda ke da budadden yanayin kasuwanci mai inganci. (Saminu Alhassan)














