Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) reshen Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) ta ayyana yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin Abuja, sakamakon rashin warware matsalolin da suka shafi ɗaukaka matsayin malamai da jin daɗinsu.
Yajin aikin ya fara ne ranar Laraba, 7 ga Oktoba, 2026, bayan wani zama da kwamitin zartarwa na shugabancin kungiyar ya gudanar a ranar Talata a Labour House, Abuja.
A cikin wata sanarwa da Shugaban NLC na FCT, Knabayi S. Adalo, ya sanya wa hannu tare da fitarwa, kungiyar ta umarci ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu da su daina zuwa wuraren aikinsu har sai an sake ba da wani umarni.
Matakin ya biyo bayan karewar wa’adin kwanaki bakwai da kungiyar ta bai wa Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) domin ya magance bukatun kungiyar da suka shafi malamai a Abuja.














