Hukumar ‘Yansandan Jihar Kano ta kaddamar da gagarumin samame a maboyar masu laifi a fadin jihar, a wani sabon yunkuri na dakile ayyukan daba a cikin birnin Kano.
Wannan aiki ya fara ne a karshen mako, inda ‘yansandan ke kokarin rushe kungiyoyin masu tada zaune tsaye da dawo da zaman lafiya a cikin birnin Kano. Sanarwar hakan ta fito ne daga mataimakin Jami’in hulda da Jama’a na ‘Yansanda, DSP Abdullahi Hussaini, a madadin Kwamishinan ‘Yansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori.
- Ganduje Ya Noƙe Kan Furta Ko Shettima Zai Yi Takara Da Tinubu A 2027
- Wakilin Sin A IAEA Ya Yi Tir Da Harin Isra’ila Kan Cibiyoyin Sarrafa Nukiliyar Iran
A cewar sanarwar, CP Bakori ya gudanar da taron tsaro na manyan jami’an ‘yansanda a ranar 14 ga Yuni, 2025, domin duba matsalar daba da tsara sabbin dabaru na yaki da ita. Ya umurci jami’an da su gudanar da aiki bisa bayanan sirri tare da kai farmaki maboyar ‘yan daba don kama su a inda suke.
Sabuwar dabarar hukumar ta hada da:
-
Gudanar da samame bisa bayanan sirri a wuraren da aka gano.
-
Karfafa hulda da al’umma da shugabannin yankuna don samun shawarwari kan inganta tsaro.
-
Ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki don samun nasara a yaki da daba.
Kwamishinan ‘Yansanda ya tabbatar wa mazauna Kano cewa hukumar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyinsu, inda ya ce za su ci gaba da more zaman lafiya ba tare da fargaba ba. Haka kuma, hukumar ta bukaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani abin da suka gani na zargi ta layukan gaggawa: 08032419754, 08123821575, ko 09029292926.
Rahotanni sun nuna karuwar ayyukan daba a Kano, musamman a cikin birnin, wanda ke janyo asarar rayuka da raunuka ga ‘yan daba da fararen hula.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp