Rundunar ‘yansanda a jihar Nasarawa ta ce tana gudanar da bincike a kan satar wani jariri da aka haifa a asibitin kwararru na Dalhatu Araf (DASH), Lafia.
Kwamishinan ‘yansandan jihar (CP), Umar Nadada ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a Lafiya.
- INEC Ta Shirya Gudanar Da Zaben Cike Gurbi A Jihar Kano
- Mai Gadi Ya Harbe Sufeton ‘Yansanda Har Lahira A Adamawa
Nadada ya bayyana cewa, wani Suleiman Abdullahi ne ya kai karar hukumar ‘yansanda a ranar Talata, 9 ga watan Janairu.
Ya ce, mutumin ya kai karar ne a ofishin ‘yansanda na A-Division Lafia, inda ya ce, matarsa ta haihu a DASH ta hanyar ofreshon (CS) a asibitin kuma an sace jaririn.
Kwamishinan ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, an kama wasu mutane uku da ake zargi inda a halin yanzu aka mika su sashin binciken manyan laifuka (CID) na rundunar da ke Lafia.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa an sace jaririn ne da aka haifa da misalin karfe 3:00 na safiyar ranar Talata, 9 ga watan Janairu, 2024 da misalin karfe 6:00 na safe.