Dan takarar shugaban kasa na jamiyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kalubalanci gwamanonin jam’iyyar APC da ke sukar tsarin saura fasalin kudi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar.
Babban Bankin Nijeriya (CBN) wanda ya kawo sabon tsarin na sauya fasalin Naira a shekarar da ta gabata ya sanya ranar 31 ga watan Janairu 2023 a matsayi rana ta karshe na karban tsofaffin kudi na Naira 200, 500 da 1000. Da aka aiwatar da dokar sai lamarin ya rika samun suka daga gwamnonin APC.
- Buhari Da Iyalinsa Sun Isa Katsina Don Yin Zabe
- Sin Ta Yi Kira Ga Al’ummar Kasa Da Kasa Da Ta Kara Mai Da Hankali Kan Batun Somaliya
Rabiu Musa Kwankwaso ya ce maganganun da gwamnonin APC ke yi a baya-bayan nan kan dokar sun ba shi mamaki kwarai da gaske, musamman yadda suke cin mutuncin shugaban kasa kai-tsaye babu sakayawa.
“Kawai sai muka ji sun buge da zagin jagorori, abun daure kai ma shi ne har da shugaban kasa, abun da ban taba kawowa za su iya aikatawa ba.
“Na yi mamakin kalaman da ke fita daga bakinsu, har na fara tunanin me ke damunsu haka? Watakila akwai kamshin gaskiya a batun da EFCC cewa suna ajiye da biliyoyin kudi a gidajensu.
“Yanzu wannan dokar ta sanya duka wani kudin sata ya zamo mara amfani, watakila abun da ya bata musu rai kenan, don haka muna farin ciki da abun da gwamnatin tarayya ta yi a wannan karon.
“Da haka nake bai wa sauran hukumomi shawara da su sanya ido kan wadannan mutanen, kuma ina so in tabbatar muku da cewa jam’iyyarmu za ta taimaka wa gwamnatin tarayya ranar zabe.
“Ku gaya wa duk ’yan NNPP su shiga EFCC, su shiga wurin da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro suke (ranar zabe), duk inda suka ga ana kokarin sayen kuri’u su hana,” kamar yadda shi Kwankwason yake fada.