Mataimakin zababben shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ziyarci garin Minna na Jihar Neja, inda ya gana da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), a ranar Alhamis.
Ya yi ganawar sirri da IBB, inda suka tattauna wasu batutuwa da ba a bayyana ba.
- Sin Ta Bayyana Adawa Da Karin Kasafin Kudaden Ayyukan Soji Na Wasu Kasashe Karkashin Manufar “Barazanar Ayyukan Sojin Kasar”
- An Fitar Da Rahoton Amurka Ta Keta Hakkin Dan Adam Na Makaurata Da Yan Gudun Hijira
Mataimakin shugaban kasan ya kuma kai wa mai martaba Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago ziyara, bayan ya bar gidan IBB da misalin karfe 3:30 na rana.
Sai dai har yanzu ba a san cikakken bayani kan ganawar tasu ba, amma LEADERSHIP, ta tattaro cewa zababben mataimakin shugaban kasar na iya kwana a Minna, babban birnin jihar, domin hada hannu da kungiyoyin masu ruwa da tsaki kafin ranar mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu.