Masu karatu barkanmu, yau shafin na mu wani muhimmin batu ya zakulo mana, wato Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU! Wannan kungiya tsawon shekaru ta dade tana zama manyan kanun labarai a manyan gidajen labarai da suka hada da gidajen talabijin, rediyo, jaridu da sauran kafofin watsa labarai a fadin Nijeriya.
Mahimmancin kungiyar ya kai matukar kololuwa a idon iyaye da ɗaliban jami’o’in Nijeriya. ASUU, kungiya ce ta Malaman jami’o’in tarayya da jihohi a fadin kasar.
Duk wani yunkuri da ka iya sanya ASUU ta yi barazanar tsunduma yajin aiki, iyaye da daliban Jami’a ba sa maraba da wannan yunkurin domin yana kawo cikas ga ci gaban karatun daliban.
Kungiyar ASUU, tana rajin kare hakkin walwalar mambobinta, da samar da ababen more rayuwa don samun ingantaccen yanayin koyarwa, inda duk wannan hakkokin take neman su a wurin gwamnati.
Don haka, kungiyar ke fafutuka da gwagwarmaya kullum a wurin gwamnati da nufin kare muradunta da bukatunta.
Wacece ASUU kuma yaushe aka kafata?
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta samo asali ne daga Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (NAUT). An kafa ƙungiyar NAUT a shekarar 1965, wadda ta ƙunshi ma’aikatan ilimi a Jami’ar Ibadan, Jami’ar Nijeriya, Nsukka, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, Jami’ar Ife, Ile-Ife da Jami’ar Legas, da ke Legas.
NAUT ta fi mayar da hankali kan kyautata yanayin hidimar mambobinta, da kuma walwalar zamantakewa da tattalin arziki da siyasa ta ƙasar. Sai dai, a cewar Attahiru Jega, ƙungiyar NAUT ba ta ɗauki wani matsayi mai muhimmanci ba kan batutuwan ƙasa ko siyasa.
A ra’ayin masana, NAUT ta fi kusa da tsarin kungiyoyi matsakaita. Ba kasafai take fitar da wata sanarwa ta bai ɗaya ba, sannan kuma, ba ta tsaurara wa gwamnati kan bukatunta saboda tausayawa gwamnatin.
Sauye-sauye da aka fara samu a ɓangaren zamantakewa ta siyasa da alkiblar tattalin arziki da kasar tafara fuskanta, wani masani Eskor Toyo, ya bayyana cewa, manufofin NAUT ba su dace da wannan zamani ba, akwai bukatar a yi mata kwaskwarima, inda ya ce gwagwarmayar kungiyar zai fi dace wa a kira ta da ASUU.
An kafa ASUU a shekarar 1978, a lokacin da kakar kasuwar man fetur ta fara raguwa, inda ƙasar ta fara girbar kuskuren shugabanninta na kin yin amfani da arzikin da aka samu na man fetur wurin kafa masana’antu domin samar da jin dadi da walwalar jama’a.
Mulkin kama-karya na soja ya yi tasiri matuka wurin gurgunta ‘yancin al’ummar Nijeriya. Fannin ilimi da jami’o’in Nijeriya suka rasa ‘yancin da suke da shi, sabida mulkin kama-karya na soja. Tallafin ilimi, da kuma na jami’o’i, ya koma ƙamas. Waɗannan abubuwan su suka kara taimakawa ASUU ta fara tsoma baki a fannin siyasa tun daga shekarar 1980.
Jagoraorin ASUU suka zama masu kaushi da tsauri ga gwamnati, inda kungiyar a lokacin ta fi damuwa da manyan batutuwan ƙasa, kuma ƙungiyar ta tsaya tsayin daka kan manufofin dakile zalunci da rashin dimokuraɗiyya na ƙasar.
…. za mu ci gaba a mako na gaba














