Masu sana’ar hada-hadar kudi na POS a Nijeriya sun koka kan yawaitar katsewar network din layukan waya daga kamfanonin sadarwa a Nijeriya inda suka misalta hakan a matsayin hanyoyin da ke janyo wa harkar kasuwancinsu koma baya.
Na’urar POS dai ya zama wani hanya mafi sauki da jama’a ke runguma wajen yin hada-hadar kudade kama daga shigar da kudadensu ko cirewa. Hakan kuma ya biyo bayan wahalar zuwa bankuna ko na’urar cirar kudi na ATM da jama’a ke fuskanta.
- Amurka Na Dauke Da Nauyin Dakatar Da Kisan Fararen Hula A Rafah
- Matsalar Tsaro A Nijeriya: Akwai Bukatar Daukar Kwakkwaran Mataki
A Nijeriya masu sana’ar POS wadanda mafi yawansu matasa ne sun kasance masu shiga tsakanin bankuna da kwastomomi inda suke saukaka wa bankuna matsalolin hulda da kudade.
A ‘yan kwanakin nan an yi ta fuskanta matsalolin da suka shafi na katsewar network daga kamfanonin sadarwa, inda masu POS suka nuna hakan a matsayin babban matsala da ke kawo musu cikas.
Wani mai sana’ar POS a jihar Bauchi, Sulaiman Alhassan ya shaida wa shafin Kimiyya da fasaha cewa, “A ‘yan kwanakin nan muna fuskantar matsalolin network gaskiya. Har ta kai idan mutum na son kada ya rasa kwastomomi yadda yake so ko yadda ya saba to dole sai ya sayi data a layuka a kalla uku, idan wannan kamfanin ya katse sai ya canza zuwa wani kamfanin sadarwa, to matsalar da muke fuskanta ko a hakan ne ma, idan kwastoma ya zo kana kokarin canza layi zuwa wani domin ka samu karfin network din da za ka tura ko cire wa kwastoma kudi, a nan gabar sai hakurin mutum ya kare ka ga ya nemi wucewa zuwa wani wajen.
“Na rasa kwastomomi sosai a irin wannan. Kuma dai daman cinikin ma ya ragu amma sakamakon matsalar network gaskiya muna rasa ciniki matuka.”
“Amma idan mutum ya dage yana da layuka da yawa kamar uku, duk da hakan ma asara muke yi, misali, idan zan sanya datar MTN na dubu uku na ci gaba da tura kudi ko cirewa, sai ya zama a kowani rana ina fargabar network zai iya dauke min, zan kuma sake wani datar dubu uku a zain ko glo ka ga ko ba komai na sake kashe wani kudin a wani abun da ban tsara yi ba.
“A zahiri yawaitar katsewar network na janyo mana cikas da matsaloli,” ya shaida.
Kazalika, wata mai sana’ar POS Mary Daniel daga jihar Gombe ta shaida cewar, “Layi daya nake amfani da shi, duk lokacin da network ya yanke sai dai na zauna na yi ta kallo. Babbar matsalar da muke fuskanta idan network din nan na yawa, za mu iya tura kudi ya zo bai je ba ko kuma ya fita bai nuna mana ba. Don haka a irin wannan fargabar kamar mu masu karamin karfi kawai na kan gwammace na hakura da cigaba da kasuwancin har sai an samu network mai karfi kafin na cigaba da yin kasuwancina. A hakan kuma asara kawai muke yi da bata lokaci,” ya shaida.