Wata mahaifiya ta kasance cikin rudani da damuwa bayan gano abin da ‘ya’yanta suka yi ma ta da kayan sana’a. Jaylynn Butler mai yin kwalliyar amare a bukukkuwa ta shiga dakin wanka a lokacin da ta gano cewa, yaranta sun yanke shawarar yin wasa da kayan kwalliyarta kuma sun lalata kayan kwalliya da na kyaran jiki masu yawan gaske, wasu ma daga ciki ba a yi amfani da su ba tukunna.
Jaylynn, wanda ke zaune a garin Wisconsin, ta yada aikin na yaran ta a cikin bidiyo man-hajar TikTok, wanda ya sanya mutane da damatsokaci akai.
Ba wai kawai sun lalata kayan kwalliyar masu matukar tsada da take amfani dasu a matsayin wani bangare na kasuwancin ta ba ne, amma kuma sun lalata gidan baki daya, zub da man shafawa da goga kayan kwalliyar a jikin bango.
A farkon sakonnin biyu game da abin da ya faru, mahaifiyar tana cewa:, “Yadda 2020 ta kare a gare ni.”
Masu amfani da TikTok sun firgita da faruwar lamarin, tare da dubunnan tsokaci kan bidiyon. Wata mata ya ce, “Da ni ce sai na yi kukan da idanuna zasu fita. Kayan kwalliyan dana na yi watanni ina tarawa an lalata shi a rana guda.”
Wani kuma ya ba da amsa, “Da fatan za ki dawo mu su da kyaututtukansu na Kirsimeti da kuma sake siyan wasu kayan shafawar, a koya mu su darasi. Ina mai bakin ciki.”
Na ukun ya rubuta, “Zan yi bakin ciki kawai idan na ji mahaifiyata tana kuka kamar haka. Iyaye ba su da yawa a wannan duniyar don haka lalata abin da suke so shi ne bai kamata ba.”