An Yi Gagarumin Bukin Kaddamar Da Jam’iyyar NRM A Abuja

Sabuwar Jam’iyya wacce Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa ta yi wa rajista, wato Jam’iyyar Ceton Al’ummar Kasa (National Rescue Mobement) ‘NRM’  ta gudanar da gagarumin bikin kaddamar da jam’iyyar da kuma bada tutoci ga shugabannin jihohin Kasar nan.

An gudanar da wannan gagarumin taro ne a Babban Filin taro na kasa dake Abuja. Taron ya gudana ne karkashin jagorancin Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Sanata Saidu Muhammad Dansadau. Dubban magoya baya ne daga sassa daban-daban na Nijeriya suka yiwa Abuja kawanya domin halartar wannan taro na kaddamarwa. A jawabin shugaban jam’iyyar, Sanata Sa’idu Muhammad Dansadau, ya bayyana cewa, Jam’iyyarsu jam’iyya ce ta ceton al’umma da hadin kan al’ummar kasa. Don haka ta gama shirinta tsaf kafin ta fito, kuma ita wannan jam’iyyar ba ta dogara da kowa ba sai Allah.

Ya ce; “Wannan jam’iyyar ta karade kasar nan, don neman hanyoyin da zai kai ta ga ci. Don haka, muna da tsarurruka talatin da muke dasu, wadanda za su amfanar da al’ummar Kasar nan.”

Sanata Dansadau ya kuma bayyana cewa; “Gazawar Jam’iyyun da suka yi mulki na PDP da APC ne ya sa mu ka fito da wannan jam’iyyar ta NRM, mai hoton Zuma, ga zaki ga magani ga kuma harbin macuta.

“Yau dan Adam a kasar nan ba bakin komai yake ba, dabba ta fi dan Adam daraja a Kasar nan. Gwamnati ta gaza kare mutuncin mutane da addininsu, da dukiyoyinsu da rayukansu. Don haka bamu ga dalilin bin ta ba. Shi ya sa muka fito da wannan jam’iyyar don cantanta. Kuma da yardar Allah wannan jam’iyyar sai ta kai gaci, domin jam’iyya ce mai mutunta dan Adam da addininsa da mutuncinsa da dukiyoyi da rayuka. Saboda haka idan al’umma suka mara wa jam’iyyar NRM baya lallai za ta fitar da su daga kuncin rayuwar da azzalumai suka jefa su a ciki.” in ji Sanata Dansadau

Shi ma baban bako mai jawabi a wurin kaddamarwar, Dike Chukwumerije ya bayyana cewa; ‘’Wannan jam’iyyar ta hada kan Al’ummar Kasar nan ce don haka kada kowa yayi zulimin shigarta, kuma da yardar Allah sai ta kawo hadin kan al’ummar Kasar. Daga yau zamu tashi babu dare, babu rana a kan fadakar da al’umma manufofin wannan jam’iyyar ta Ceton Al’ummar Ka. Kuma wannan jam’iyyar Babu ruwanta da bambancin jinsi, ko addini. Domin kuwa al’ummar Nijeriya ‘yan kasa daya ne babu wani bambancin a tsakaninsu.

Shi ma Babban bako Mai sharhi kan kundin littafin Jam’iyyar, Alhaji Bubba Galadima ya bayyana cewa; “Wannan taro, taro ne na Jam’iyyar NRM, Kuma na zo ne don kashin kaina, domin in yi lancin wannan litafin da zai zama shaida ga al’ummar kasar nan. Kuma na yi mamaki jam’iyyar da aka yi wa rijista ba ta wuce wata biyu da yin rijista ba amma ta tara gagarumin taron da jam’iyya Mai kansila ko gwamna ba su iya hada irin wannan taron. Don haka wannan jam’iyyar ya kamata a jinjina mata. kuma ga dukkan alamu za ta kai ga ci.

Wannnan Jam’iyyar Mai samfirin Zuma ga zaki ga harbi. Ba zata bar duk wanda ya zalunci al’umma ba, sai ta harbe shi. Kuma wannan littafin na da manufofi masu kyau da ci gaban kasa. Don haka nake jinjina wa wadanda suka shirya wannan littafin.

“Wasu za su yi mamakin cewa ina jam’iyyar APC, ina cikin kwamitin zartaswa na kasa baki daya, kuma ina daga cikin mutane tara da suka sanya hannu aka yi wa jam’iyyar APC rajista,don haka don ina jam’iyyar APC, ba zan yi gaba ba, gyara muke so mu kawo, ba gaba a cikin  siyasa ba. Wannan ne dalilina na zuwa wannnan taro, a kashin kai na.”

Buba Galadima ya karkare da cewa, “wannan jam’iyya ta NRM ta mori shugaba, domin Sanata Dansadau na sanshi sama da shekaru 40 a gwagwarmayar siyasa. Ba ya cuta, sannan ba ya zama da macuci. Kuma kudi ba su sayansa, don haka duk jam’iyyar dake da irinsu Dansadau a cikinta, za ta kai gaci.

Shugaban jam’iyyar na jihar Zamfara, Alhaji Danbuba Muhammad , jim kadan bayan amsar tuta ya bayyana wa ‘yan jaridu cewa; “Wannan tuta ce ta ceton al’umma, mai son kawo canji a kasar nan. Kuma za ta fid da al’umma cikin kuncin rayuwa. Don haka za mu shiga birane da kauyuka don bayyana wa al’umma manufofinta, a jiharmu ta Zamfara.”

Shi ma jigo a Jam’iyyar NRM, Alhaji Lawali Lakwaja Anka ya bayyana cewa, Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta, kai da ganin wannan taron da kuma wadanda ke cikin jam’iyyar, take ka san juma’armu karbabbiya ce. Sai dai mu yi Shirin amsar mulki da yardar Allah, tunda shi ne ke bayar wa. Kuma gare Shi muka dogara, kuma zai bamu.” in ji shi.

Exit mobile version