Jam’iyyar APC reshen Jihar Yobe, ta sha alwashin daukaka kara kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Damaturu, Jihar Yobe, ta yanke wa Bashir Sheriff Machina, a matsayin wanda ya dace ya tsaya takarar Sanatan Yobe ta Arewa a zaben 2023.
Jam’iyyar ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin duk da hukuncin da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, wanda a halin yanzu ke kan kujerar Yobe ta Arewa a majalisar dokokin kasar, ya amince da hukuncin da kotun ta yanke.
- Wadanne Abubuwa Ne Ake Iya Fasa Aure Saboda Su?
- Matakan Farfado Da Masana’antun Fatu Na Haifar Da da Mai Ido A Nijeriya —Shugaban NILEST
Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Mohammed Gadaka, ya ce jam’iyyar ba ta amince da hukuncin ba.
Gadaka, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya ce Lawan ya ci gaba da zama dan takarar jam’iyyar a zaben Yobe ta Arewa a 2023.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Muna sane da hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Damaturu, babban birnin Jihar Yobe ta yanke a ranar Laraba, 28 ga Satumba, 2022, game da zaben Sanatan Yobe ta Arewa da ke tafe.
“Duk da haka, cikin girmamawa mun yi watsi da matakin da Shugaban Majalisar Dattawa, Mai Girma Sanata Ahmad Lawan ya dauka na amincewa da hukuncin da kotun ta yanke wanda ya haramta masa tsayawa takara da kuma shiga zaben.
“A bisa hakkinmu na shari’a, jam’iyyar APC reshen Jihar Yobe ta yanke shawarar daukaka kara kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke domin alfanun Jihar Yobe da Nijeriya da kuma shugabanci na gari, dole ne mu kare tare da dorewar Sanata Ahmed Lawan. -Shekaru asharin da uku wanda ya yi abin koyi a matsayin dan majalisa da kuma tarihinsa na shugabanci da kishin kasa – da kuma jajircewarsa na ganin Nijeriya ta yi aiki.”
Idan za a tunawa a ranar Larabar da ta gabata ne mai shari’a Fadima Murtala Aminu, ta babbar kotun tarayya da ke Damaturu a Jihar Yobe, ta ayyana Machina a matsayin dan takarar Sanatan Yobe ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC.
Alkalin ta kuma umarci jam’iyyar APC da ta mika sunan Machina ga INEC a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani a Yobe ta Arewa.
Alkalin ta yi watsi da zargin zaben fidda gwani, inda shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya fito a matsayin dan takarar sanata a matsayin wanda ya lashe zaben.
Lawan wanda ya halarci zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC kuma ya sha kaye a hannun Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, daga bisani ya tafi neman tikitin takarar kujerar sanatan yankinsa, matakin da Machina ya kalubalanci shi, inda ya bayyana cewa ya shiga zaben fidda gwani na Jihar Yobe ta Arewa, kuma ya lashe zaben.
Da yake mayar da martani kan hukuncin kotun a wata sanarwa a ranar Alhamis, shugaban majalisar dattawan, ya ce ba zai daukaka kara kan hukuncin ba, kuma ya amince da Machina a matsayin wanda ya cancanta ya yi takarar Sanatan.