Yobe Ta Bayar Da Gudummawar Naira Miliyan 50 A Ginin Masallacin Mai Potiskum

Masallacin

Daga Muhammad Maitela,

Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da gudumawar naira miliyan 50 a asusun ginin sabon masallacin a Potiskum, wanda ya gudana ranar Asabar a fadar Mai Potiskum.

Da yake jawabi a kaddamar da neman taimakon gina masallacin, Gwamna Mai Mala Buni ya ce, “Zan yi amfani da wannan lokaci, a madadin baki dayan al’ummar Jihar Yobe wajen bayar da gudumawa ta naira miliyan 50. Haka kuma da karin wasu miliyan 10 da wani na kusa dani yace na bayar a madadin sa.”

Har wala yau, Gwamna Buni ya karfafa gwiwar mahalarta taron wajen bayar da tasu gudumawa a aikin alherin komai kankantar sa- daidai karfin kowane mutum, Allah zai kalli niyyar kowane mutum.

Tun daga bisani, Alhaji Auwal Abdullahi, shi ne babban mai kaddamar da taimakon ginin masallacin wanda masarautar Potiskum ya shirya, wanda ya bayar da gudumawar naira miliyan 50 tare da kira ga masu bayar da taimakon su guji alkawarin karya.

A nashi bangaren, shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya bai wa gidauniyar ginin masallacin tallafin naira miliyan 20 da na miliyan 7 a madadin sanatoci uku da suka raka shi wajen taron.

Wasu da suka bayar da gudumawa a wajen taron sun hada da Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya aiko da naira miliyan 10, Sanata Adamu Aleiru, naira mikiyan 5, Sanata Ibrahim Geidam naira miliyan 10, Santa Ibrahim Bamai naira mikiyan 10, Alhaji Aliko Dangote naira mikiyan 10, Sanata Ali Modu Sheriff naira miliyan 10.

Exit mobile version