Muh'd Shafi'u Saleh" />

Za A Bai Wa Matasa 500 Horo Kan Sana’o’i A Adamawa

Arewa

A wani shirin samar da aikin dogaro da kai ga matasa, gwamnatin jihar Adamawa za ta bada horo kan sana’o’in dogaro da kai ga matasa dari biyar.

Matasan 500, za su samu horo ne kan sana’o’in baba, kiwon kifi, kaji, aikin abinci, adana, ado, daukan hoto, sabulu, hada sola da kuma intanet.

Gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana haka lokacin da ya ke kaddamar da shirin da sashen yaki da talauci da samar da aikinyi Poberty Allebiation and Wealth Creation Agency (PAWECA), ta shirya a Yola.

Haka kuma gwamnan ya ce zai bada fili mai fadin kadada 100 a kowace karamar hukuma ga matasan, da ya ce hakan zai ba su damar baje irin baiwar da Allah, ta yadda jihar za ta amfana da shi.

Ya ce, “gwamnati na kokarin ganin ta rage aikata munanan ayyuka, kamar kungiyoyin yara ‘yan shila, masu garkuwa da mutane, da masu haifar da tashin hankali, yanzu sun ragu, samun abinyi zai rage aikata munanan ayyuka” in ji gwamnan.

Da itama ke jawabi shugaban sashen kirkiro da sana’o’i da rage fatara PAWECA Hajiya Aishatu Bawa Bello, mutum dubu biyu (2000) za su samu horon, amma saboda matsalar Korona an raba su kashi-kashi a kananan hukumomin jihar 21, ta ce sashin ya bai wa matasa 420 horo.

Haka shi ma shugaban ofishin majalisar Burtaniya da ke Yola Abdulkadir Bello Ahmed, ya bayyana farin ciki da shirin gwamnatin jihar, ya ce damace ga matasa ta yadda su ma za su dogara da kansu.

Exit mobile version