Hukumar zaben Kasar Nijar CENI ta sanar da cewa za a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar Nijar. An cimma wannan matakin ne saboda babu jam’iyyar da ta ci kashi 50 ko fiye da haka na kuri’u.
Kamar yadda jadawalin hukumar zaben ya nuna, ranar 21 ga watan Fabrairun 2021, ne za a gudanar da zagaye na biyun. Sakamakon zaben da hukumar ta bayyana yanzu ya nuna cewa dan takarar jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarraya, Bazoum Mohamed, shi ne ya lashe kashi 39,33 cikin 100, inda yake da kuri’a 1, 879, 000.
Sai kuma Mahamane Ousmane na jam’iyyar RDR Canji da ya lashe kashi 16.99 cikin 100 kuma ya samu ƙuri’a 811,838. Hakan na nufin za a fafata zaɓen zagaye na biyu tsakanin ‘yan takarar guda biyu, wadanda su ne kan gaba a zagayen farko.