• English
  • Business News
Sunday, July 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Za A Samu Mamakon Ruwan Sama Da Hazo Daga Litinin Zuwa Laraba A Nijeriya

by Abubakar Sulaiman
2 months ago
in Labarai
0
Za A Samu Mamakon Ruwan Sama Da Hazo Daga Litinin Zuwa Laraba A Nijeriya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hukumar hasashen yanayi ta ƙasa (NiMet) ta fitar da hasashen sauyin yanayi na kwanaki uku, inda ta bayyana cewa za a fuskanci ruwan sama da hadari tun daga Litinin zuwa Laraba a sassa daban-daban na Nijeriya.

A cewar NiMet, ranar Litinin za a samu hazo da ruwan sama da safe a wasu sassan jihohin Taraba, Kaduna, Gombe, Bauchi, Kebbi, Sokoto, Katsina, Jigawa da Kano a Arewa. Daga bisani a rana, za a ci gaba da samun hadari da ruwan sama a jihohin Taraba, Kaduna, Sokoto, Borno, Kebbi da Zamfara.

  • Noman 2025: Dole Ne Manoma Su Kiyaye Hasashen Hukumar NiMet
  • Zafin Rana Zai Tsananta A Wasu Jihohin Nijeriya – NiMet

A yankin Arewa ta tsakiya, jihohin Abuja, Neja da Nasarawa za su fuskanci ruwan sama da hazo da safe. Yamma kuma za a samu hadari da ruwan sama a Filato, Abuja, Nasarawa, Kwara, Neja, Kogi da Benue.

A Kudu, za a fara da samun gajimare da ruwan sama a wasu sassan Ondo, Ogun, Edo, Ebonyi, Abia, Cross River, Rivers da Akwa Ibom. Daga bisani kuma, ana sa ran ruwan sama a Oyo, Ekiti, Osun, Lagos, Edo, Imo, Enugu, Delta da Bayelsa.

Ranar Talata, NiMet ta ce za a fuskanci hazo da ruwan sama da safe a jihohin Kano, Zamfara, Katsina, Bauchi, Gombe, Adamawa, Borno, Yobe da Taraba. Yamma kuma, za a samu ruwan sama a jihohin Taraba, Kebbi, Borno, Adamawa, Kaduna da Bauchi. Arewa ta tsakiya za ta ci gaba da hadari da ruwa a Abuja, Neja da Nasarawa, yayin da jihohin Kogi, Kwara da Filato za su bi sahu da rana.

Labarai Masu Nasaba

VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Ranar Laraba, ruwan sama da hazo za su afkawa jihohin Zamfara, Adamawa, Kaduna, Sokoto, Kebbi da Taraba. Daga baya kuma, za a samu ruwan sama a jihohin Katsina, Bauchi da Sakkwato. Arewa ta rsakiya za ta fuskanci ruwan sama a Abuja, Nasarawa, Neja da Binuwe da safe, yayin da yamma za ta shafi Nasarawa, Filato, Kwara da Kogi.

A Kudu, ana hasashen ruwan sama da safe a Ogun, Ondo, Oyo, Edo, Enugu, Ebonyi, Cross River, Rivers da Akwa Ibom, sannan daga bisani a rana, za a sami ruwan sama a fadin yankin.

NiMet ta gargjama’a su ɗauki matakan kariya, musamman inda hadari zai faru, domin iska mai ƙarfi na iya gabatar da haɗari. An shawarci mutane su guji tuƙi a lokacin ruwan sama mai ƙarfi, su cire na’urori daga soket, su guji tsayuwa kusa da manyan itatuwa, sannan masu jirgin sama su nemi rahoton yanayi daga NiMet kafin tafiya. Ana kuma shawarci jama’a su dinga bin sahihan bayanan yanayi daga shafin NiMet:

www.nimet.gov.ng.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: NiMetRuwa
ShareTweetSendShare
Previous Post

Jirgin Sojoji Yayi Kuskuren Buɗe Wuta Kan Ƴan Sa Kai A Maru

Next Post

Babu Wanda Zai Iya Kora Ta Daga PDP —  Wike

Related

VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace
Labarai

VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

8 minutes ago
Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 
Wasanni

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

9 hours ago
Kasar Sin Na Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantu A Gaza Tare Da Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta
Labarai

Isra’ila Na Sanya Alamar Rusau A Dubban Gidajen Fararen Hula A Gaza

12 hours ago
Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson
Siyasa

Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson

14 hours ago
An Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
Manyan Labarai

An Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja

15 hours ago
‘Yancin Gashin Kai: Ma’aikatan Kananan Hukumomi Sun Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki
Labarai

‘Yancin Gashin Kai: Ma’aikatan Kananan Hukumomi Sun Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki

17 hours ago
Next Post
Babu Wanda Zai Iya Kora Ta Daga PDP —  Wike

Babu Wanda Zai Iya Kora Ta Daga PDP —  Wike

LABARAI MASU NASABA

VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

July 27, 2025
Yadda Ake Faten Acca

Yadda Ake Faten Acca

July 27, 2025
Hanyoyin Gyaran Gashi

Hanyoyin Gyaran Gashi

July 27, 2025
Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

July 26, 2025
Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

July 26, 2025
Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

July 26, 2025
Kasar Sin Na Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantu A Gaza Tare Da Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta

Isra’ila Na Sanya Alamar Rusau A Dubban Gidajen Fararen Hula A Gaza

July 26, 2025
Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

July 26, 2025
Ruwan sama

Natijojin Auren Dattijo Ga Budurwa

July 26, 2025
An Yi Bikin Karbar Fitilar Gasar Wasannin Kasa Da Kasa Ta Shekarar 2025 A Chengdu

An Yi Bikin Karbar Fitilar Gasar Wasannin Kasa Da Kasa Ta Shekarar 2025 A Chengdu

July 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.