A gobe Jumaa ne za a wallafa makalar babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, mai bayani game da matakan bunkasa dukkanin sassa, da aiki tukuru wajen aiwatar da jagorancin jamiyyar kwaminis bisa karfin kanta, bisa babban mizanin inganci da karin matakai na tabbatar da nasarar hakan.
Za a wallafa makalar ta shugaba Xi, wanda shi ne shugaban kasar Sin kuma jagoran kwamitin kolin rundunar sojin kasar, a muhimmiyar mujallar nan ta Qiushi ta kwamitin kolin JKS fitowa ta 20 a bana. (Saminu Alhassan)
ADVERTISEMENT














