Gwamnatin kasar Denmark ta dauki aniyar haramta kona Alkur’ani Mai Tsarki a bainar jama’a bayan jerin kone-konen da suka haddasa yamutsi a kasashen Musulmai.
Ministan shari’ar kasar, Peter Hummelgaard ya ce irin wannan mataki na kona Alkur’ani ya cutar da Denmark kuma ya sanya al’ummarta cikin hatsari.
- Gwamnan Kaduna Ya Bude Masaukin Dalibai Mai Gado 400 Da Ofishin Hukumar Raya Birnin Zariya
- An Kaddamar Da Shirin Baje Kolin Inganta Harkar Noma Da Sana’o’i A Kano
Dokar wadda ake shirin kafawa za ta mayar da duk wani matakin wulakanta Alkur’ani ko Littafin Bayabul, matsayin laifi da za a iya hukunta mutum, ta hanyar cin tara ko dauri a gidan yari tsawon shekara biyu ko sama da haka.
Gwamnatin kasar mai sassaucin ra’ayi ta ce tana son aika wani sako ga al’ummar duniya.
Ministan harkokin waje, Lars Lokke Rasmussen ya ce Denmark ta shaida jerin zanga-zanga har 170 cikin ‘yan makonnin nan, a ciki har da kona Kur’anai a gaban ofisoshin jakadancin ksashen waje.
Hukumar leken asirin Denmark ta yi gargadin cewa al’amuran da suka faru a baya-bayan nan sun tsananta barazanar kai harin ta’addanci.
Ita ma kasar Sweden mai makwabtaka ta shaida jerin kone-konen Alkur’ani kuma jami’an tsaronta sun yi gargadin cewa al’amuran tsaro za su tabarbare. A watan Yuli, masu zanga-zanga sun cinna wuta kan ofishin jakadancinta a Iraki.
Sai dai duka kasashen Denmark da Sweden sun jinkirta daukar mataki a kan kone-konen saboda dokokinsu na sassaucin ra’ayi a kan ‘yancin fadar albarkacin baki.
A shekarun 1970 ne Sweden ta soke dokarta ta haramta sabo. Gwamnatin birnin Copenhagen ta yanke shawarar daukar mataki bayan karin kone-konen Alkur’ani a karshen watan Yuli cikin Denmark da Sweden.
Kungiyar Kasashen Musulmai ta Duniya (OIC) ta yi kira ga mambobinta su dauki matakan da suka dace a kan kasashen da ake wulakanta Alkur’ani.
Ministan shari’ar ya dage a kan cewa kudurin canza dokar ba zai shafi furuci ko rubutun bayyana albarkacin baki ko zanen shagube ba. Sai dai ya ce kona littattafan addinai ba su da wata manufa sai haifar da baraka da haddasa gaba.
“Wani ginshikin al’amari ne ga tsarin dimokradiyyarmu cewa mutum na da ‘yancin fadar albarkacin bakinsa,” a cewar Mataimakin firaminista Jakob Ellemann-Jensen. “Kuma ya kamata mutum ya rika sara, yana duban bakin gatari.”
Denmark ba za ta tsaya ta zuba ido kawai ba a lokacin da irin wadannan abubuwa masu nakasu ga tsaron kasar ke faruwa, ya kara da cewa.
Firaministan Sweden, Ulf Kristersson, ya ce gwamnatin Stockholm ba za ta dauki irin wannan mataki na makwabciyarta ba, saboda hakan mai yiwuwa zai bukaci yi wa tsarin mulkin kasar garambawul.
Ministan shari’ar Sweden Gunnar Strommer ya fada wa manema labarai cewa shawarar sake nazari kan dokar tabbatar da kwanciyar hankalin jama’a, ta yi daidai.
Gwamnatin kasar na son canza dokar domin ta haramta tarukan da za su yi barazana ga tsaron al’ummar Sweden.
Ministoci a Denmark sun kuduri aniyar yi wa dokar sauye-sauye ranar 1 ga watan Satumba, sannan su gabatar da sauye-sauyen ga majalisar dokoki don zatarwa kafin karshen wannan shekara.
Ana sa ran, haramcin za a yi shi ne a sashen kundin aikata laifuka da ke hana ‘yan kasar muzanta wata kasar waje, ko tutarta da sauran wani tambarinta.