Kungiyar kwadago ta Kasa ta sha alwashin yin fito na fito da gwamnatin tarayya a kan yunkurin da sabon shugaban kada, Bola Tinubu ke yi na janye tallafin mai.
Kungiyar ta ce ba za ta amince ba, saboda janye tallafin zai jefa al’umma a cikin wahala.
- Akwai Wadataccen Mai Da Zai Ishi ‘Yan Kasa Nan Da Kwanaki 30 —NNPCL
- Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Dakta Idris Abdulaziz
Tun bayan sanarwar da shugaba Tinubu ya yi a ranar da aka rantsar da shi aka fara dogayen layukan mai a sassan kasar nan.
Kwamarade Nasir Kabir shi ne sakataren tsare-tsare na Kungiyar NLC ya shaida wa manema labarai cewa shugaban ya yi hanzarin sanar da shirin cire tallafin man fetur ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba.
“Kafin ka janye tallafi sai ka kawo wutar lantarki, tituna duk sun wadata talakawa sun rabu da talauci a kasa, ake maganar gwamnati ba ta hannu a cikin wannan abu”, in ji shi.
Kungiyar ta yi ikirarin a cikin sa’o’i bayan sanarwar shugaban kasa al’ummar kasar nan sun tsinci kansu cikin wani hali na tsaka mai wuya saboda an fuskanci karancin man fetur a wasu sassan kasar nan da karin farashin mai inda a wasu gidajen mai farashin man fetur din ya karu da kashi 300 cikin 100.
Mahukuntan kasar nan sun sha ikirarin cewa wasu tsiraru ne ke amfana da tallafin man, don haka ya kamata a cire shi.
To sai dai NLC ta yi watsi da haka kamar yada Kwamared Nasir Kabir ya bayyana.
“Duk wannan magana ne ina tabbatar maka tatsuniya ce, ba mu gamsu da shi ba, ai maganar gaskiya shi ne me ya sa su gwamnatin da ta shigo da ke son ta janye wannan tallafi, da mun zauna mun nuna mu su aubuwan da ke kasa, sai su gane cewa mun fi su gaskiya sai su fasa”, in ji shi.
Kungiyar kwadagon ta ce tana adawa da wannan mataki na shugaba Tinubu kuma ta nemi gwamnati da ta janye shirin cikin gaggawa.
NLC ta kuma yi ikirarin cewa abubuwan da wannan mataki zai haifar za su yi illa ga fanin tsaro da walwalar jama’a.