Za Mu Dukufa Tattaunawa Da Dattawan Inyamurai Da Yarabawa – ACF

ACF

Daga Mahdi M. Muhammad,

Dangane da tayar da zaune tsaye da wasu matsalolin tsaro, Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta ce, tana shirin ganawa da shugabannin kungiyoyin inyamurai ta ‘Ohanaeze Ndi Igbo’, ‘Afenifere’ da ta dattawan kudu maso kudu.

A halin da ake ciki dai kungiyar ta tabbatar da tsaron Inyamurai da ke zaune a Arewa kuma ta yi kira ga shugabannin kudu maso gabas da su ma su tsawatar don a daina kai hare-hare a kullum tare da kashe talakawan Arewa da ke zaune suna kasuwanci a kudu.

Wadannan na kunshe ne a cikin sanarwar da ACF ta fitar a karshen taronta na majalisar zartarwa ta kasa (NEC) wanda aka gudanar a hedikwatarta da ke Kaduna jiya Laraba.

 

Sanarwar wacce Shugaban kungiyar kuma tsohon Ministan aikin gona, Cif Audu Ogbe ya karanta, ta kuma bayyana farfado da ilimin makiyaya da ikon cin gashin kan kananan hukumomi a matsayin maganin matsalar kalubalen tsaro da ke addabar Nijeriya.

 

Kungiyar ta ACF ta nuna farin cikinta game da tsayawar shugabannin Kudu maso gabas da gwamnonin baya-bayan nan a kan tashin hankalin neman raba Nijeriya da kungiyar ‘yan awaren biyafara (IPOB), da kungiyar tsaro ta gabas suke yi, inda suka barranta kansu da masu ikirarin.

 

A cewar Ogbe, kungiyar ta yaba wa gwamnonin Arewa biyu, Sanata Atiku Bagudu na jihar Kebbi da Farfesa Umara Zulum na Borno a matsayin shugabannin zartarwa na jiha wadanda suka nuna bajinta a fagen yaki da ta’addanci a jihohinsu, sannan suka bukaci sauran gwamnonin Arewa da su yi makamancin wannan jaruntaka wajen yaki da rashin tsaro da ke lalata duk wani abu a Arewa.

 

Ya ce, “taron ya kuma yaba wa jarumtakar sojojinmu wadanda ke ci gaba da kasada da rayukansu a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda da masu tayar da kayar baya.”

 

Dangane da tayar da zaune tsaye, shugaban na ACF ya ce, “kungiyar ta nuna gamsuwa game da jajircewar kwanan nan da Shugabannin Kudu maso gabas da Gwamnoni suka yi game da tashin hankalin neman raba Nijeriya da ‘yan IPOB da kungiyar tsaro ta gabas ke yi. Kungiyar ta nuna farin cikinta na cewa, Dattawan Ibo a karshe sun yi watsi da masu son tayar da zaune tsaye tare da yin kira ga dattawan da su dauki kwararan matakai don ganin irin wadannan maganganun sun zo karshe.

 

Ya kara da cewa, “ACF ta lura cewa Shugabannin Kudu maso gabas sun yi kira ga shugabannin Arewa su kare ‘yan asalinsu da ke zaune a Arewa. Muna so mu tabbatar masu cewa duk Ibo da ke zaune a Arewa ana basu tabbacin tsaron kansu, wani lokacin suna jin dadin tsaro wanda ko ‘yan Arewa basa jin dadinsa.”

 

“A wani bangaren kuma, muna samum rahotanni a kullum na ‘yan Arewa, ‘yan kasa na gari wadanda ke samun lamuran su na yau da kullum a matsayin masu yankan farce, masu yin suya, masu gyaran takalmi, masu sayar da albasa, ana cin zarafin su, ana dukansu har ma ana kashe su. Muna fatan wadannan talakawan Arewa a basu irin kariyar da muka baiwa ‘yan Kudu maso gabas a tsakanin mu,” in ji shi.

 

Ya ce, “Nan gaba kadan, Dandalin na fatan ganawa da shugabannin Ohanaeze Ndi Igbo, Afenifere da shugabannin Kudu maso Kudu don tattauna batutuwan da ke ci gaba a kasar wadanda ke neman tayar da kabilu da yanki a tsakaninsu.”

 

Game da tattalin arziki, Ogbe ya ce, “kungiyar ta yi nadama kan yawan kudaden ruwa da ake karba a kan rancen bankuna a kasar. Ribar da bankuna ke karba akan lamunin kasuwanci sun yi yawa ta yadda maimakon inganta kasuwanci, suna kashe duk kamfanonin kasuwanci na asali.”

 

“Babu wani kasuwanci da zai yi aiki a Nijeriya ko a wani wuri ba tare da yanayin kawancen bayar da rance daga bankuna ba. Muna kira ga gwamnati da ta sa baki saboda durkushewar kasuwanci yana da nasaba kai tsaye da rashin aikin yi da rashin tsaro.”

 

“ACF na son yaba wa Gwamnatin tarayya kan kokarin da take yi na inganta yanayin kayayyakin more rayuwa a kasar. Gaskiyar ita ce, har ila yau, yankin arewacin kasar, tare da mafi girman yanki sama da kashi 75, kuma mafi yawan jama’a tabbas ba su samun kaso mai tsoka na sabbin abubuwan more rayuwa da ake habakawa.”

 

Kungiyar ba ta yi farin ciki da karancin kula da Jihohi da Gwamnatin tarayya ke ba kasar ba. Kiwon dabbobi kadai yakai kashi 7 na GDP, kuma yana kashe dala 1.6 kan shigo da madara ita kadai. Idan aka yi amfani da kiwon dabbobi sosai zai iya cetar da Nijeriya, wannan babban kashe-kashe ne.

 

“Yan Najeriya da yawa basu san cewa wadanda suke harkar kasuwancin dabbobi ba su da kansu suna fama da rashin tsaro na shanunsu, inda ake yawan sace shunun, kuma ana sace su ne don neman kudin fansa suma.

 

Dangane da karamar hukumar, ACF ta nuna rashin jin dadinta, ba a bar matakin gwamnati ya yi aiki ba kuma gazawar na haifar da illa ga harkar tsaron kasar.

 

Ta ce, “dole ne a ba su damar yin aiki, kuma ACF ta yi kira sosai ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihohi da su ba karamar hukumar damar gudanar da ayyuka da da aka tsara su bisa tsarin mulki don yin su. ”

Exit mobile version