Za Mu Kara Azama Don Tabbatar Da Jin Dadi Da Walwalar Malamai –Gwamna Inuwa

Makiyaya

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa gwamnatinsa tana sane da irin muhimmiyar rawar da malamai da aikin koyarwa ke takawa wajen ci gaban al’umma, don haka gwamnatin tasa za ta tabbatar da suna samun horo yadda ya kamata, da bunkasa walwalar su, da samar da muhimman ababen da ake bukata don bunkasa aikin su da samar da nagartattun dalibai.

 

A sakon sa na fatan alkhairi don alamta bikin ranar malamai ta duniya ta bana dauke da sanya hannun daraktan yada labaran gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli, Gwamna Inuwa, ya yaba da gagarumar gudunmowa da sadaukarwar da malamai ke bayarwa wajen ci gaban kasa, ta hanyar bada ilimi da kyautata makomar dalibai duk kuwa da irin dimbin kalubalen da sashin ke fuskanta.

 

Gwamnan ya bayyana taken ranar ta bana, wato ‘Malamai ginshikan farfadowar ilimi’ da cewa ya dace kuma ya zo akan gaba, duba da irin jajircewar su a irin wannan mawuyacin hali na annobar korona.

 

Yayin da yake yabo da jinjina ga malamai a yayin wannan bikin, Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada cewa gwamnatin sa zata ci gaba da daukan duk matakan kyautata walwalar malamai da ci gaban su dama karfafa musu gwiwa a jihar.

 

Sai ya bayyana malamai a matsayin kafar da yara manyan gobe ke samun haske da kyakkyawan buri da hangen nesa a yayin da suke girma.

 

Gwamnan ya ce Gwamnatin sa ta kafa cibiyar horar da malamai a Kwami, tare da karfafa alaka da hukumomi da kungiyoyi da nufin sake fasali da farfado da sashin don bunkasa hazakar su da kara musu kwarin gwiwa.

 

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce dokar ta bacin da tun farkon zuwan sa mulki ya ayyana, ya yi ta ne da nufin farfado da sashin baki daya, kama daga ma’aikata da kayan aiki don samar da nagartaccen sakamako, yana mai cewa matakin tuni ya fara haifar da da mai ido a matakan firamare da sakandare.

Exit mobile version