Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule ya sanar da cewa Gwamnatin Jihar Nasarawa ta tanadar da hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin yiwa yara Fyade.
Gwamnan ya bayyana haka sa ilin da ya karba bakwancin Membobin hukumar yaki da fasa-kauri mutani wanda aka fisanin da NAPTIP a ranar Littinin a gidan Gwamnati dake garin Lafia.
Ya ce mun jin dadi da Hukumar NAPTIP ta zabe jihar Nasarawa a matsayin wurin da za ta gina makarantar horar da Membobin ta na yammacin Afirka dabaru da ilumin zamani da yadda ake dakile harkokin fasa-kaurin mutani.
jihar ta cancanci daukar nauyin irin wadannan wurare galibi saboda kusancinta da babban birnin tarayya.
Ya kuma tabbatar da NAPTIP na cigaba da tallafawa Gwamnatin sa. Sule ya ce tuni Gwamnati na neman wani filin da za a gudanar da aikin a karamar hukumar Karu.
Gwamnan ya ba da tabbacin cewa da zarar an samar da filin, Gwamnati za ta yi masu katanga nan take.
Gwamna Abdullahi Sule ya kara da cewa; a “Jihar Nasarawa, mun riga mun sanya hannu kan dokar yaki da fyade tun a bara mun fara aiki a kan haka. Mun kuma sanya hannu kan duk kariya ta yaro da kuma cin zarafin mata,”
Gwamnan ya tabbatar da cewa tare da irin wadannan dokokin, gwamnatin jihar a shirye take ta yi aiki da NAPTIP.
Da yake kaddamar da kwamiti mai kula da fataucin mutane a jihar, Gwamna Abdullahi Sule ya nuna kwarin gwiwa cewa kwamitin za tayi aiki kafada da kafada da kowa.
Tun da farko a nata jawabin Darakta Janar na NAPTIP, Hajiya Imaan Sulaiman Ibrahim, ta bayyana cewa Hukumar NAPTIP tana shirye-shiryen kafa makarantar horar da dalubamta na yammacin Afirka a nan jihar Nasarawa.
Yayin da take yaba wa Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, kan tallafa wa hukumar don gudanar da ayyukanta, ta NAPTIP Hajiya Imaan Sulaiman , ta mika godiya ta musamman ga Gwamnan jihar Nasarawa kan yadda ya karbi hukumar hannun biyu biyu da bada goyon baya wajen shirinta na samar da tsangayar Ilumi a yankin.
Ta kara da cewa tawagar ta ziyarci jihar Nasarawa ne, domin hada giwa da Gwamnati, wajen dakile yaduwar fataucin mutane da kwararar bakin haure ba bisa ka’ida ba a jihar da ma duk kasa baki daya.
Ta kuma kara da cewa NAPTIP na hada gwiwa da Gwamnatocin jihohi, domin kafa wasu kungiyoyin kwadago karkashin kulawar Gwamnonin jihohin, don kara karfafa kokarin dakele miyagun ayyuka.
A bangare guda NAPTIP na kokarin kafa wasu kwamitocin jihohi uku a jihar Nasarawa da Jihar Benue da jihar Plateau a cikin wannan mako.
NAPTIP DG, ta yaba da yadda aka kaddamar da mambobi 19 na Jihar Nasarawa da zasu tin kari ayyukan fataucin mutane.
Ta ce kungiyar tana da Babban Mai Shari’a na Jiha da Kwamishinan Shari’a a matsayin Shugaba, yayin da Kwamandan Zonal na NAPTIP zai kasance a matsayin Mataimakin Shugaban Hukumar.