Za Mu Yi Tsayin Daka Har Sai An Inganta Ilimin Mata Da Yara A Bauchi -Hajiya Suwaiba

HAJIYA SUWAIBA JIBRIN Ita ce shugaban sashin kula da ’yancin dan adam na kungiyar nan mai fufatukar inganta ilimi da lafiya da kuma tallafa wa jama’a wato (ACTION AID). A cikin hirarta da manema labarai, ta shaida cewar sun himmatu wurin ganin an tabbatar da aiki da muradin inganta ilimin mata a Jihar Bauchi, wanda SDGs suka rattaba hannu a shekara ta 2017. KHALID IDRIS DOYA ya halarcitattauawar, ga abin da ya dauko mana:

A kwanan nan ne kuka gayyaci wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suka hada da ma’aikatan gwamnati, ilimi da kuma kungiyoyi masu zaman kansu da suke nan Bauchi. ko zaki yi mana karin haske kan abin da kuke neman cimmawa?

Kungiyar ‘ACTION AID’ ta jima tana aiki a Jihar Bauchi kusan shekaaru 13 muna aiki a wannan jihar.muna aiki a kananan hukumomi biyu, kwamiti goma muke aiki a ciki. Amma babban ayyukan da muka fi mayar da hankali, shi ne wurin gani mun bi hanyoyin da yara da ’yan mata sun samu ilimin da ya dace. A shekaru biyun da suka wuce gwamnati ta sanya hannu kan dokar da aka kafa na Hukumar Cimma Muradun Karni (SDG’s). Shi wannan aikin ba wai a ma Nijeriya ne kadai aka fara ba, a bisa haka ne muke sanya ido wajen ganin ayyukan basu tafi irin wanda aka taba yi a baya ba, muna sanya ido ne, domin tabbatar da ingancin wannan kudirin. A wannan karon mun so a fara aikin da wuri, mu sanya hanu kuma mu hada kai da kungiyoyi masu zaman kansu don cimma nasarar da aka sanya gaba, namu aikin mu tallafa wa kungiyoyi masu zaman kansu a yankunan da suke domin su ne suka san halin da talakawan yankinsu ke ciki wajen ganin an biya musu hakkokinsu yadda ya kamata kana kuma an kau da talauci a cikin al’umma.

Wannan hadin kai da muka yi mun so ne mu ga, tun da shekaru biyun nan da aka ce an sanya hanu a wannan SDGs an kafa ofis an samar da motoci an yi kaza kuma ga kudaden gwamnati an fara aiki da su. Shin me aka fara aiwatarwa a Jihar Bauchi, ba Jihar Bauchi kadai ba zamu duba Jahohin Ibonyi da kuma Delta da sauran jahohi amma zamu rarraba kafa wasu zasu duba wasu yankunan daban-daban. Wannan shine dalilin kayyatar wadannan kungiyoyin domin mu zaga cikin yankunan don ganin ayyukan da aka yi ko wanda ake son a yi. A takaice dai muna son ne mu tabbatar da sanin meke a kasa.

A wannan jihar ta Bauchi sai mu ka zo muka hada kai da wadannan kungiyoyi masu zaman kansu muka ce to bari mu gane su kansu SDGs din me suke yi, kuma ya yanayin dangantarsu da sauran ma’aikatu. Baya ga Jihar Bauchi, jihohi shida zamu duba, kuma a jahohin zamu duba kowace karamar hukuma akalla daya-daya, da kuma kauyuka dai-dai a cikin kowace karamar hukuma domin mu tabbatar da me ke akwai.

Mun samu labarin cewar Jihar Bauchi ta zabi wannan shekara na 2017 wajen ba da hankali kan kudiri na hudu (Goal 4) wanda ke kokarin tabbatar da ilimin yara, ilimi kuma ingattacce a tsakanin birni da karkara, ilimi kuma ga dukkanin yara mace da na miji, nakasashshe da wanda ba nakasashshe ba, da kuma samar da malamai da suka dace, ajujuwa, kayyakin aiki da dai sauransu. Bandaki (ba-haya) su ma a samar da su kuma masu inganci. Da suka ce wannan suka sanya a gaba sai mu kuma muka ce to bar muma mu fuskanci hakan, sai dai muna da korafin cewa idan za a hada wannan muradi na (4) dole ne a duba har da na 5. Wanda aka ce akwai rage yawan nuna banbance-banbance a tsakanin mace da na miji, yawanci an fi sanya maza a makaranta akan mata, koda matan sun samu ilimin ba a barinsu su yi aikin da shi. Bayan da muka duba haka, sai muka ce bar mu hada kai da ma’aikatun da wannan lamarin ya shafa da su kansu SDG’s din baki daya. Ka ga ke nan dukkanin bangarorin kare ’yancin jama’a sun hadu sai muka ce a je a duba a gano me ake ciki.

A binciken da kuka gudanar da wadannan tawagar naku me kuka iya ganowa ya zuwa yanzu?

Abun da muka gano ya zuwa yanzu gaskiya ba’a fara aiki ba; domin abu guda da ake ciki wanda aka fara samun nasara shi ne kawai ciyar da yara a makaranta, duk da shi ma akwai matsalolin da ake samu amma dai sai mu ce Alhamdullah an dai fara wannan. Sannan kuma a wasu makarantun da muka bibiya akwai malamai wasu kuma gaskiya babu, in ma dai akwai zaka samu basu isa ba. wasu kuma zaka samu basu da ilimin koyarwar yadda ya dace. babban matsalar da aka fi samu shi ne na ajujuwan karatu da su kansu ma rashin makarantun, wasu makarantun babu bayan gida (ba-haya) wasu kuma sun rushe, wasu makarantu kuma ginin ma basu kai matakin a koyar a ciki ba. sannan ba’a samar da yanayin da nakasassu zasu samu ilimi ba, inda ake dan samu tsiraru shine guragu wadanda za su iya zuwa makaranta, su ma fa babu wani tanadin da aka yi musu na musaman. Makarantun da dama babu yadda za a yi a koyar, wasu makaratun a kasa suke koyarwa, wasu ma a waje idan an yi ruwa sai dai a ce babu karatu wa dalibai. Wasu lokutan ka samu malamai biyu dalibai sama da dari biyu. Gaskiyar magana kan wannan kudiri da aka rattaba wa hanu ba’a fara aikinsa ba a Jihar Bauchi.

Sannan kuma muna sanya ido kan yanayin samun ilimin su mata, ta yadda mace za ta samu ilimin da yadace, yawancin garuruwan da kwamitin nan suka zaga korafin da ake samu shi ne na hana mata zuwa makaranta, idan ma sun shiga sun fara lokaci kalilan za a ciresu sai a yi musu aure. Ban ce aurar da su babu kyau ba, amma ilimin shi ma abu ne mai kyau da bukatar a barsu suke kammala Primary ta yadda zasu samu zarafin ci gaba nan gaba in sun samu zarafi.

Hajiya ya yanayin dangantar su SDG’s sauran ma’aikatu wadanda ya kamata a ce suna gudanar da aiki kusan daya?

Gaskiya a wannan bangaren fa akwai gyara sosai da ya kamata a yi, domin koda aka ce an fitar da group 4 sashin ilimi ke nan, a tsakanin hukumar ilimin jihar da SDG’s, babu wani alamar a zama domin tattaunawa, kamar ma’aikatar ilimi basu ma san da wannan kudurin ba. bayan su ma babu wani zama da ake yi a tsakanin hukumar cimma muradun karni da wasu ma’aikatu kan cimma wannan kudirin, bamu samu labarin wannan ba har zuwa yanzu. Bamu sani ba ko akwai wani zaman da suke yi bayanin ne bai zo mana ba. amma gaskiya babu wani tsari. Da yawan mutane suna korafin cewa daga sashin gwamnatin tarayya da na jaha babu wani tsari da zaka ga an turo da aiki daga gwamnatin tarayya na a shiga wasu yankuna a yi aiyuka. Daga can tarayya sukan rubutu ma’aikatar ilimi don su bada rahoton abun da aka kawo. An bamu misali gwaggwara guda daya, wasu tallafin da aka kawo daga tarayya aka shiga da su aka ce a bayar, amma takardun turo aikin ba’a samu takaimaimen ina aka kai littafan nan ba; da kayan koyon sana’a na mata dukka an nemi inda aka kai an rasa. Idan har gwamnatin tarayya zata kawo kwaligila kai tsaye kawai su shiga domin yin aiki, alhali ma’aikatun da ya dace su sani basu ma sani ba, misali an kawo wani aiki ta bangaren ilimi a ce ma’aikatar ilimi na jaha basu sani ba, ko tallafin lafiya, ma’aikatar lafiya basu sani ba, ko na rowan-sha amma ma’aikatar da ke kula da wannan basu sani ba ka ga an rinka yin shiririta kenan. Domin kuwa wasu lokutan akan zabi wasu yanki a yi ta yi musu hidima a maimakon a tsara yadda kowa ma zai mori tallafin, in sun kawo aiki daga tarayya su bincike ma’aikatar da ke kula da wannan domin a kauce wa nanatawa aiki a waje guda don saura ma su amfana.

Ta bangaren kungiyar iyaye da al’umman gari (SBMC) wadanda aka kafa da zasu ke duba su wadannan makarantun ya alakarsu da SDG’s a bincikenku?

Matsalolin biyu ne, an kafa kungiyar iyaye da al’umman gari (SBMC) don su ke sanya ido kan wannan aikin, su kungiyar nan sun fito ne daga irin shirin PTA da ake sanya al’umma don cimma wani abu. To, su jama’an basu dauki aikin da muhimmanci sosai ba; duk da an ce ana tura musu wasu kudade don su ke gyara dan wasu abubuwan da suka lalace, to gaskiya a zaman da muka yi bamu ga aikinsu ba. amma hotunan da aka baje a wajen ayyukan da suke jibge sun fi karfin wannan kungiyar. su kudin da ake basu idan falange ya bule ne sai su gyara, kofa ta karye su gyara, to matsalolin su fi wannan gine-ginen ma babu balle a zo a iyi irin wannan gyaran, domin wasu makarantun an fara aiki ba’a karasa ba, babu rufi nan gaba idan aka barsu haka zasu koma gidan beraye da kwari ne.

To, mene ne kuke son cimmawa a halin yanzu?

Babban burinmu mu dai shi ne talaka ya gani a kasa, domin in an ce hukumar cimma muradun karni akwai yaye talauci, tabbatar da ilimi ingattacce a samar da ruwan sha mai kyau a kuma tabbatar da kawo tsaro da sauransu. Duk wadanda suka fi wahalar nan sune talakawa musamman wadanda suke cikin kyauyuka da kananan hukumomi a nan dukkanin damuwowi suke jibge, don haka a irin wadannan wajajen ne muke neman mu ga canji ya samu. Abubuwan da muke son mu cimma za mu baiwa gwamnati hadin kai sosai a tsakanin SDG’s da kuma su ma’aikatun gwamnati domin a samu hadaka. An ce za a yi aiki da (GOAL 4) a wannan shekara ta 2017, bangaren ilimi har yanzu ba’a kawo tsarin da aka turo daga gwamnatin tarayya, waye me yin tsarin? Daga can gwamnatin tarayya za a yi ko kuma daga jihar ne za su yi?. Tun da an riga an sanya hanu jahohi su dauki nauyin abunsu, kudaden da ake son a yi aiki da su  a kan SDGs ba wai ana maganar wai kudade su shigo  daga wasu wurare bane fa; idan wasu kasashe sun kawo tallafi ne, kudadenmu na kasa da su ake amfani a wannan sashin.

Wasu lokutan za ka samu ga aiki nan SDG’s na jiha suna yi, sannan kuma sai ka ga na Tarayya ma suna yin aikin irin wannan, yaya wannan lamarin ke damunku?

Matsalar da ke faruwa dai duk rashin tsarin nan ne ke jawo irin wannan, idan suka da tsari ba za ake samun irin wannan matsalar ba. zamu dai yi roko a garesu da su yi aiki tsakani da Allah su kuma tabbatar da tsarin nan wajen gudanar da aiki domin talaka ya mora ribar da ya dace.

 

Exit mobile version