Zababben gwamnan Jihar Katsina, Umar Dikko Radda, ya ce tsaro ne zai zama babban jigon gwamnatinsa, idan ya dare karagar mulki daga ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Juma’a bayan ya mika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari takardar shaidar lashe zabe tare da gwamnan Jihar Katsina mai barin gado, Aminu Bello Masari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Mutum 14 Sun Shiga Hannun ‘Yan Sanda A Kano Kan Aikata Fashi Da Makami
- Taron Kolin Demokuradiyya Na Amurka Ya Shaidawa Duniya Ma’auni Biyu Da Amurka Ta Dauka Kan Batun Demokuradiyya
A cewarsa, idan babu zaman lafiya da tsaro, ba za a samu ci gaba ba.
Ya ce, “Eh, na sha fadin cewa tsaro shi ne fifikonmu. Wannan shi ne abin da za mu mayar da hankali sosai a kai domin sai an samu zaman lafiya da tsaro ne za a iya zuwa gona, da makaranta, da asibiti, har ma da kasuwa.
“Don haka tsaro muhimmin abu ne a ci gaban tattalin arzikin kowace al’umma. Sannan noma na daya daga cikin manyan hanyoyin samar da ayyukan yi a jiharmu kuma yanki ne na rayuwar al’ummarmu, don haka dole ne mu samar da tsaro ga al’ummarmu.
“Kuma mun yi alkawarin shigar da ‘yan kasa kuma mun yi alkawarin sanya amfani da fasahar zamani wajen magance matsalar tsaro a jiha ta.”
Dikko ya kuma ce ya zo ne domin gode wa shugaban kasa kan nasarar da jam’iyyar APC ta samu a jihar.
“Muna so mu fara aikinmu nan take bayan an rantsar da mu a matsayin gwamna da mataimaki. Don haka ina ganin muna yin komai a yanzu don ganin mun sanya komai inda ya dace domin mu kai gaci nan da nan bayan an rantsar da mu”.
Da aka tambaye shi ko wace shawara ce shugaban kasar ya ba shi, Radda ya ce: “Shugaban ya kasance yana bayar da shawarar tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin gwamnati.
“Kuma a ko da yaushe ya bukace mu da mu yi adalci ga Allah Madaukakin Sarki wajen sauke nauyin da ke kanmu. Kun san yana da matukar muhimmanci ku fahimci cewa baya ga tambayoyin manema labarai, ban da tambayoyin al’ummar Jihar Katsina, Allah Ta’ala zai tambaye ku idan kun hadu da shi. Don haka ina ganin za mu yi aikinmu da kyau kuma za mu tabbatar da cewa mun kasance masu gaskiya da rikon amana ga al’ummar Katsina gwargwadon iyawarmu.”