Wani matashin dan siyasa mai suna Alhaji Hamisu Zakiru Kusfa a Zariya da ke Jihar Kaduna ya bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya cancanci ya zama shugaban kasar Nijeriya duba da kishin da yake da shi.
Alhaji Hamisu ya ci gaba da cewa duk cikin wadanda ke neman shugabancin Nijeriya a zaben 2023, babu wanda yake nuna damuwarsa ga al’ummar Nijeriya, musamman ‘ya’yan talakawa kamar Kwankwaso.
A cewarsa, idan an dubi yadda a shekarun baya ya dauki nauyin karatun ‘ya’yan talakawa zuwa kasashen tare da sisin kwabon iyayen yaran ba.
Ya kara da cewa tarihi ba zai manta da Kwankwaso ba, na yadda a shekarun baya ya za ga jihohin da suke kudancin Nijeriya wajen ganawa da matan da aka kashe wa mazan a dalilin wani yamutsi da ya faru tare da ba su tallafin kudade domin su sami abin da za su ciyar da marayun da aka bar masu.
Ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su yi karatun ta-natsu wajen zaben shugaban kasa mai zuwa a badi. Ya ce babu wanda zai iya tunkarar matsalolin Nijeriya kai-tsaye, sai Kwankwaso.