Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabimaila ya bayyana dalilan da suka sa wasu ‘yan majalisa na tarayya suka fadi a zaben fid da gwani da aka kamala.
Ya ce tsarin daliget ne ya sa mafi yawancin ‘yan majalisa suka sha kaye a zaben fid da gwani da aka gudanar.
Gbajabimaila ya bayyana dalilan ne lokacin da yake jawabin maraba a ranar Talata, ya dora laifin faduwar na ‘yan majalisar a kan tsarin zabe na daliget wanda wasu jam’iyyu suka yi amfani da shi wajen fitar da dan takara.
Ya kara da cewa ‘yan majalisa za su ci gaba da yakar tsarin zabe na wakilai saboda sun ga illar hakan.
Idan dai za a iya tunawa, majalisa ta amince da kudurin dokar zabe wanda ya tilasta wa jam’iyyun siyasa su gudanar da zaben fid da gwani ta hanyar ‘yar tinke.
Amma sai dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da kudurin, inda ya bijiro da wasu hanyoyi na gudanar da zaben fitar da gwani.
Ya ce, “Mafi yawancin ‘yan’uwanmu ‘yan majalisa sun fadi a zaben fitar da gwani sakamakon wannan tsari na daliget, mun dai yi watsi da wannan tsali a zauren majalisa tun da dadewa. Tsarin zabe na daliget bai kamata a ce shi ake amfani da shi a cikin siyasar Nijeriya ba,” in ji shi.
Ya sha alwashin cewa zai tattauna da dukkan shugabannin majalisar wakilai a kan wannan lamari.
Haka kuma shugaban majalisar wakilan ya bukaci gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ta damke wadanda suka kai hari a cocin Owo da ke cikin Jihar Ondo.
Ya kuma kara yin alwashin cewa ‘yan majalisa za su gudanar da bincike kan dukkan kasafin kudi na shekara uku da suka gabata. Ya ce majalisa za ta tabbatar da cewa an amince da dukkan kudurin da suka shafi kundin tsarin mulki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp