Connect with us

LABARAI

Zaben PTD Reshen Kaduna : An Sake Zabar Abduraheem 63 Shugaban A Karo Na Biyu

Published

on

An sake zabar Kwamarade Abdurahim Haruna 63 a matsayin Shugaban kungiyar direbobin tanka PTD reshen jihar Kaduna karo na biyu, inda shi da sauran zababbun yan majalisarsa, zasu sake shafe shekaru hudu kan shugabancin kungiyar.
A hirarsa da manema labarai a Kaduna Abdurahim Haruna 63 ya ce, muna yiwa Allah godiya da ya nuna mana wa’adin mulkin mu na farko har zuwa karshensa, inda kuma yayan kungiyar, suka zake zabar mu karo na biyu don ci gaba da shugabancin su.
Ya ce, sakamakon barkewar annobar Korona uwar kungiyar ta kasa ta yanke shawarar ya kamata ayi mitin na musamman a rantsar damu, inda aka rantsar damu a shalkwatar uwar kungiyar ta kasa dake a Abuja.
A cewar Abdurahim Haruna 63, bamu wuci yayan kungiyar su ashirin ba da suka halarci rantsarwa ba kuma bayan mun dawo jihar Kaduna, muka mikawa gwamnatin jihar da jami’an tsaro takardar rantsar damu don su tabbatar da an gudanar da zaben.
Abdurahim Haruna 63 ya ci gaba da cewa, ina mai kira ga daukacin yayan kungiyar PTD reshen jihar Kaduna kada su gajiya kan goyon bayan da suke bamu, musamman don ciyar da rayuwar su da kuma kungiyar gaba, nusamman don a kara samar da ci gaba mai dorewa.
Abdurahim Haruna ya yi alkawarin cewa, zaici gaba da janyo yayan kungiyar a jikinsa don a gudu tare a kuma tsira tare, ina kuma fatan zasu ci gaba da bamu goyon bayan su kamar yadda suka saba.
Shugaban kungiyar Abdurahim Haruna 63 ya kuma yabawa Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed el-rufai kan goyon bayan da yake baiwa kungiyar ta PTD reshen Kaduna, inda ya ce, daga Allah sai kuma Gwamna el-rufai, musamman kan zaman lafiyar da aka samu a cikin kungiyar reshen jihar.
Wasu daga cikin yayan kungiyar Abdullahi Musa dan Gara, Alhasan Amadu Unguwar Dosa, Usman Hassan da kuma Suleiman Jibrin duk sun yaba kan yadda aka gudanar da zaben a cijin kwanciyar hankali da lumana.
A cewarsu, zamu ci gaba da bai wa sababbin shugabannin kungiyar goyon bayan da ya dace don su dora daga inda suka tsaya kan shugabancin su, inda suka ce, abinda muke bukata ne Allah ya bamu kuma a lokacin zangon mulkin Shugaban kungiyar Abdurahim Haruna 63 na farko, babu wata hayaniya a kungiyar.
Sun bayyana cewa, an gudanar da zaben a cikin kwanciyar hankali da lumana, inda suka yi nuni da cewa, ba’a taba yin zaben da muka samu butsuwa ba a kungiyar sai a wanan karon kuma a shirye muke mu bai sababbin shugabannin kungiyar, musamman shugabanta Abdurahim Haruna dukkan goyon bayan da ya dace don ci gaba da ciyar da yayan kungiyar da kuma kungiyar gaba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: