Musa Muhammad" />

Zabukan 2019: Matasa A Yi Hattara Da Miyagun ’Yan Siyasa (II)

Alhamdu lillahi, yau ma Allah cikin ikonsa ya kawo mu wani makon, inda muke yin bayanai na jawo hankali game da matasa ta yadda za su zama na nagari, su daina bari ana amfani da su wajen aikata barna, musamman a zamantakewar al’umma don samun ingantacciyar rayuwa da za a amfani juna.
A yau ma dai za mu ci gaba ne da bayani a kan wannan maudu’i namu. Amma a yau zan dan surka da wani bayani da wani rubutu da wani mai karatunmu ya rubutu mani bayan da ya karanta rubutun da na yi a makon da ya gabata, inda ya yaba, kuma ya yi fatan alhairi. Ga abin da yake cewa.

Assalamu alaikum. Bayan dubun gaisuwa da fatan alhairi gare ka. Mun gode, mun gode, mun gode. Na rubuto maka wannan sako ne domin in nuna maka matukar godiyata game da rubutun da ka yi mai take a sama, wanda aka buga a makon da ya gabata, inda ka jawo hankalin matasa game da shiga bangar siyasa, musamman a zabe mai zuwa. Ba abin da za mu ce illa mu gode maka, tare da fatan Allah saka da alhairi ya biya ka ladan wannan aikin alhairi da ke yi.
Bayan haka, ni ina ganin irin wannan nasiha da ke yi wa matasa, ya makata ka samu wani gidan rediyo ka rinka magana, domin abubuwan da kake rubutawa suna da muhimmanci, kuma ina ganin zai fi yaduwa in da a ce a rediyo ne, domin mafin yawan matasan da ake yin rubutun nan domin su, ba sa karanta jarida, amma suna sauraren rediyo.
Gaskiya ni ma matasan kasar nan suna ba ni mamaki matuka, musamman yadda za ka gansu ana amfani da su wajen shaye-shaye, inda ake hayarsu wajen bangar siyasa. Wani abin takaici, sai ka ga matasa, wasu ma har da aurensu, amma sun lalace sun bari ana amfani da su wajen wannan mummunan abu, yawancinsu babu ilimin addini ko na boko.
Ni matashi ne kuma kurma, amma alhamdu lillahi na dogara da Allah, ina neman abin da zan ci in sha, domin yanzu haka ina sayar da shayi ne, wanda shi ne nake yi nake samun abin rufin asirirna, har na yi aure, ina da ’ya’ya uku, a haka na yi, ba tare da na samu taimakon ko sisi daga wajen ’yan uwana ba.
Ina fadin wannan ne domin ni Jaridarku ta LEADERSHIP A YAU ba ta taba wuce ni ba, kowane mako ina saye ba tare da na ji wani abu ba, ina matukar samun ilimi sosai a ciki.
Saboda haka wannan jawo hankali da kake yi wa matasanmu abu ne da zai taimaka matukar matashi yana son abin da zai amfane shi a rayuwarsa ta duniya da lahira.
Ni a nan ina bin bayanka wajen yin kira ga matasa su tashi su nemi na kansu, kar su sake a yi amfani da wajen bangar siyasa ko wani abin da bai dace ba. Matasa mu sani mu ne ginshikin kowace al’umma, don haka akwai bukatar mu himmatu wajen gyara halayenmu ta yadda za mu zama abin koyi nan gaba.
A karshe ina yi maka fatan alhairi, Allah ya ba ka nasara a duk abin da ka sa a gaba, ya kareka daga sharrin makiya da mahassada.
Sako daga Sa’idu Adamu, Runji Dakwa, gidan Sarkin Fulani Runji Bwari, Abuja

To, Malam Sa’idu na gode, kuma lallai ai kai ma a wannan rubutu naka ka yi abin da ya dace, domin kai ma ai ka yi wa matasan nasiha. Sai dai mu yi fatan Allah sa matasa su ga wannan rubutu da idon basira, su kasance masu bin hanyar da ta dace wajen harkokinsu.
A makon da ya gabata, ga wanda ya samu karantawa, zai tuna cewa na yi bayanin cewa a halin da muke ciki dai mun shiga shekarar da za a gudanar da zabubbuka a kasar nan, kuma kamar yadda aka sani, wasu miyagun ’yan siyasa na nan sun kafa tarko, wadanda in dai suka ga ba za su ci zabe ba, to za su tabbatar sun jangwalo ta yadda za ta shafi kowa, kuma ba da kowa za a yi amfani ba, sai da matasa.
Don haka ne nake cewa yana da muhmmanci matasa su yi karatun ta-natsu, su san inda yake masu ciwo, kar su sake irin wadannan miyagun su yi amfani da su. Domin kamar yadda kowa ya sani ne, irin wadannan mutane ba sa sanya nasu matasan a gaba a duk lokacin da suke son aiwatar da irin wadannan abubuwa, tamkar su ba su da matasan ne.
Har nake cewa wani hanzari ba gudu ba, a wani rubutu da na yi baya na kwo tsokacin cewa, sana’a ga matasa ta zama wajibi bisa la’akari da halin da ake ciki a duniyarmu ta yau. Domin ba za a iya cewa gwamnati za ta iya sama wa kowane matashi aikin yi ba, ko da kuwa ya yi karatu zuwa na Digiri ne ko gaba da Digiri, ballantana kuma matasahin da bai samu halartar makaranta ba.
Na kawo wannan ne domin mu fahimci irin muhimmancin da sana’a ke da shi a rayuwar matashi. Domin idan matashi yana da sana’a, to ba yadda za a yi a ce masa ya ajiye sana’arsa ya zo a ba shi dan wani abu dan kalilan don ya je ya yi wata barna ta dukiya ko ta rayuka.
Hakika idan ya zama matshi ba shi da sana’a, to shi mugu zai iya bullo masa ta duk inda ya ga dama domin ya yi amfani da shi wajen biyan bukatun kansu. Ya ba shi kudi kalilan da kayan maye ya ingiza shi. Amma babu wata hanya ta gyaruwar matashi kamar samun sana’ar dogaro da kai, ta hanyar dogaro da kai ne ake samun matashi natsattse, wanda babu ruwansa da shiga duk wani tashin hankali ko aikin da bai dace ba.
Abin da ya sa na kawo batun zaben da ke tafe a wannan rubutu nawa shi ne, saboda bisa la’akari da abubuwan da suka faru a baya, inda aka yi amfani da irin wadannan matasa wajen kashe rayuka tare da barnata dukiyar mutane haka kawai. Ba za mu manta da abin da ya faru a zabukan da suka faru a shekarun baya ba, inda aka sa wasu matasa suka rinka kona dukiyar al’umma.
Wani abin bakin ciki takaci, idan irin wadannan miyagun ‘yan siyasa da muke magana a kai sun yi amfani da matasan wajen cimma burinsu, shikenan sun gama da su, ba ruwansu da duk abin da zai same su, ya zama ‘tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa ka-duka.’ Masu uwa a murhu ne me kawai wasu sukan ke ofishin da aka kama su karbo su, shi ma ba don komai ba sao don idan wani aikin ya taso. Amma idan matashi ya ji rauni ko mutuwa, ba ruwnsu da shi.
Ga ma wani kyakkyawan misali, wannan matashi da ya rubuto mani wannan sako, ya bayyana mana cewa shi kurma ne, amma yana san’a, da wannan sana’ar ce ya yi aure har ma yana da zuriyya.
Saboda haka yana da muhmmanci ya zama kowa yana da sana’arsa, ta yadda matashi ko da yana karatun Jami’a ne, to ya zama idan ya samu hutu akwai inda zai je ya yi sana’a, ballantana kuma a ce ba ya zuwa makaranta. Domin ita harka ta makaranta ba kowa ba ne ke da dama ko halin samun zuwa, amma sana’a fa? Kowa yana da hali da daman zuwa, matukar Allah ya ba shi lafiya.

Exit mobile version