Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya ce, muddin aka zabeshi a matsayin shugaban kasa a 2023, zai iya shawo kan dukkanin matsalolin da suke addabar kasar nan.
Tinubu ya kara da cewa zai yi amfani da sabbin na’urorin zamani na Kimiyya wajen yaki da matsalar tsaro tare da yakar ‘yan bindiga dadi, ‘yan ta’adda da sauran matsalolon tsaro muddin ‘yan Nijeriya suka bada nasu goyon bayan ta hanyar zabinsa, ya kuma ce, babu wani yanki na kasar nan da zai sake fama da matsalar tsaro.
Tsohon gwamnan Jihar Legas din, ya nuna kwarin guiwarsa na cewa zai yi nasara a zaben 2023 da ke tafe da zai gudana a shekara mai zuwa.
Tinubu ke cewa: “Ina da karsashin da zan iya magance dukkanin matsalolin da suke addabar qasar nan tare da daidaita alakar kasar bisa turbar da ta dace.”
Tinubu, wadda ke jawabi a wajen taron tattalin arziki da zuba hannun jari karo na 7 na jihar Kaduna (KADINVEST 7.0) ya kare da cewa gwamantinsa za ta tabbatar da inganta sashin kasuwanci tare da samar da hasken wutar lantarki yadda ya kamata a kasa baki daya.
Ya ce, tabbas al’ummar Nijeriya za ji dadin gwamnatinsa domin a shirye yake ya hidimta wa kasar domin lamura su samu dawowa yadda ya kamata.
“Za mu toshe kafofin sata da handame dukiyar al’umma domin tabbatar da gaskiya da adalci,” a cewar Tinubu.
Tinubu wanda ya samu rakiyar Gwamnonin Jigawa da Kebbi da wasu kusoshin jam’iyyar APC zuwa wajen taron a Kaduna.