Zan Yi Kokarin Taimakawa Faransa Ta Lashe Kofin Turai –Benzema

Benzema

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma tawagar ‘yan wasan kasar Faransa, ya yi alkawarin cewa zai yi iya yinsa wajen ganin tawagar kasar Faransa ta lashe gasar cin kofin nahiyar turai da a yanzu haka ake bugawa a kasashe daban-daban.

Dan wasa Benzema ya bayyana cewa ya yi farinciki da ya ci wa tawagar kasar ta Faransa kwallaye biyu a gasar Euro 2020, bayan da suka tashi 2-2 da Portugal ranar Laraba wanda hakan ya sa kasar ta karkare wasannin rukunin a mataki na daya

Dan wasa Cristiano Ronaldo ne shima ya zura biyu a ragar Faransa a bugun fenareti da hakan ya sa ya yi kan-kan-kan da Ali Deai na Iran mai tarihin yawan ci wa tawaga kwallaye a duniya da kwallaye 109.

Kwallon da Benzema ya ci a bugun fenareti itace ta 28 da ya ci wa tawagar Faransa, tun bayan kusan shekara shida rabon da ya buga mata kwallo sakamakon shari’ar da yake fuskanta a kasar.

A rukuni na shida da suka yi wasan karshe ranar Laraba, Faransa za ta buga wasan kusa dana kusa dana karshe wato kuarter finals da kasar Switzerland a gobe Litinin 28 ga watan Yuni da za su kara a filin wasa na Arena Național .

Portugal mai rike da kofin za ta kece raini da Belgium, wadda take ta daya a jerin wadanda ke kan gaba a buga kwallo da  zasu  yi wasan a yau Lahadi 27 ga watan Yuni a Estadio La Cartuja.

Kasar Jamus kuwa za ta buga karawar daf da na kusa da na karshe da Ingila a filin wasa na Wembley ranar Talata 29 ga watan Yuni duka a kokarin da kasashen sukeyi na ganin sun lashe gasar.

Exit mobile version