Wata kungiyar masana mai suna ‘The Centre for the Promotion of Pribate Enterprise (CPPE)’ ta bayyana cewa, zanga-zangar tsadar rayuwa da matasa ke gudanarwa a sassan kasar nan yana da matukar illa ga tattalin arzikin kasa musamman ganin halin gargara da tattalin arzikin ke ciki.
Shugaban kungiyar, Dakta Muda Yusuf ya sanar da cewa, zanga-zangar zai yi wa tattalin arzikin kasa illar da zai kai ga asarar Naira Biliyan 400 a kullum in har ba a dauki mataki ba.
- Tura Ta Kai Bango, Zanga-zanga Ta Kai Gidan Buhari Da Sarkin Daura
- Bata-gari Sun Cinna Wa Sabon Ofishin NCC Wuta A Kano
Ya kara da cewa, wannan asarar zai matukar girgiza tattalin kasa, musamman gann a kwai yiwuwar haifar da tarnaki ga bangarori da dama na tattalin arzikin kasa.
Dakta Yusuf, ya ce, bangarorin da za su fi dandanawa sun hada da saye da sayarwa, masana’antu, shakatawa, sufuri, bankuna, otal-otal, aikin gona, zirga-zirgan jiragen sama da kuma bangaren gine-gine. “wannan kuma ya hada da yiwuwar asarar rayukan al’umma da dukiyoyin al’umma da kuma barnatar da dikiyoyion al’umma da za a iya rasawa. Kaddarorin gwamnati na kuma cikin garari.”
Daga nan ya kuma yaba wa Babban Sufeton ‘Yansanda a kan yadda ya amince da hakkin ‘yan kasa na gudanar da zanga-zanga inda ya kuma yi alkawarin samar da kariya ga masu zanga-zangar.
“Muna kira ga masu zanga-zanga da su hada hannu da jami’an tsaro domin a yi zanga-zangar a kuma kammala lafiya ba tare da tashin hankali ba.
“Yana da matukar muhimmanci a gudanar da zanga-zanga cikin natsuwa da kwanciyar hankali ta haka za a isar da sakon da ake bukata ga hukuma,” in ji shi.
Ya kuma yi kira masu shirya zanga-zangar da su dakile bata gari wadanda basu yi wa kasar nan fatan alhairi daga shiga ga cikin zanga-zangar, “Dole mu hada hannu domin kare dukiya da kaddarorin kasarmu daga hannun ‘yan baranda wanda fatan su shi ne takurawa al’umma ta kowacce hanya, bai kamata mu yarda bata gari su yi amfani da mu ba.”