Da sanyin safiyar yau Alhamis ne aka gurfanar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gaban kotun Kofar Kudu da ke birnin Kano.
Tun da farko Mai shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola, ya ce ya gamsu da shaida da hujojjin da aka gabatar masa game da karar da ake yi wa Abduljabbar na yin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.
- Budurwa Ta Roki Kotu Ta Tilasta Tsohon Saurayinta Ya Biya Ta Bashin 180,000 Da Ta Ke Bin Sa
- Majalisar Dattawa Ta Bukaci CBN Ya Sake Nazarin Dokar Takaita Cirar Kudi
Ya ce hujojji sun bayyana cewar Abduljabbar ne ya kirkiro dukkanin wadannan kalamai a cikin karatunsa.
Don haka kotun ta same shi da laifin aikata aifin da ake tuhumarsa da shi wanda aka shafe watanni 15 ana shari’a.
Sai dai lauyan Abduljabbar ya nemi kotun da ta yi masa sassauci saboda a cewarsa sabanin fahimta aka samu dangane da neman ilimi.
Sai dai Abduljabbar ya ce ba da yawunsa lauyan nasa ya nema masa sassauci ba, inda ya mike a kotun ya ce ba ya bukatar a masa sassauci, a shirye yake ya karbi duk irin hukuncin da za a yanke masa.
Yanzu haka dai ana dakon jiran hukuncin da alkalin kotun zai zartawar da Abduljabbar.