Zazzaɓin cizon sauro: Wata Ƙungiya Ta Raba Magani Kyauta A Kano

Daga Abdullahi Muhammad Sheka

An bayyana buƙatar da ake da ita na ganin al’umma sun shigo cikin harkokin lafiya domin haɗa hannu da hukumomi don tallafawa harkar lafiya a ƙaramar hukumar Kumbotso, wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar wayar da kan matasa da harkokin siyasa (Kumbotso Youth awareness Forum) Alhaji Maikuɗi Muhammad Sheka (Shugaba) a lokacin ƙaddamar da shirin duba marasa lafiya, musamman masu fama da cutar zazzaɓin cizon sauro da halin yanzu ake fama da ita a Jihar Kano.

Alhaji Maikuɗi Shugaba ya ce, yau watanni uku kenan da kafa wannan ƙungiya waccce ta ƙuduri aniyar tallafawa al’ummar ƙaramar hukumar Kumbotso, inda suka shirya tare da ƙaddamar da shirin duba marasa lafiya a asibitoci uku  da ke wannan ƙaramar hukuma ta Kumbotso.

Shugaban ya ce, ’ya’yan ƙungiyar ne suka haɗa kuɗi; mai taro mai sisi aka sayi waɗanann tarin maggunguna da a halin yanzu ake rabawa marasa lafiya. Ya ce, likitoci 16 mazauna ƙaramar hukumar Kumbotso ne suka ɗauki nauyin zaga asibitocin domin duba marasa lafiyar da basu magani kyauta.

Ya ci gaba da cewa yanzu haka an fara da asibitin Sheka, mako mai zuwa za a wuce asibitin Chalawa daga nan kuma sai na Mariri.

Farfesa Garba Ibrahim Sheka na sashen tsumi da tanadi na Jami’ar Bayero ta Kano ne ya ƙaddamar da raba magungunan kyauta, a jawabinsa ya tabbatar wa da jama’a cewa lokaci ya wuce da za a jira sai gwamnati ce za ta yi wa jama’a abin da suke buƙata, saboda haka Farfesan ya tabbatar wa da al’umma samun goyon bayansa, musamman gashi ya na cikin iyayen wannan ƙungiya.

Shugaban Sashen Lafiya ta ƙaramar Kumbotso, Hajiya Hajiya Zainab Usaini ta bayyana cewa tun zuwanta ƙaramar hukumar Kumbotso yau shekara guda ba ta taɓa ganin irin wannan hidimar arziki ba.

Ta ce, wannan ya na daga cikin kiraye-kirayen da hukumomin lafiya ke yi domin jama’a su haɗa ƙarfi domin tallafawa al’umma. Shugabar ta buƙaci jama’a su daina zuwa ɗakunan sayar da magani kaitsaye da zaran sun kamu da wata cuta, musamman ma bisa la’akari da cewa, zazzaɓin cizon sauro ba a  bada magani har sai an yi gwaji.

Hajiya Zainab Usaini ta yi kira ga masu hannu da shuni da su tallafa wa wannan ƙungiya don ci gaba da wannan abin alheri.

Kansilan Lafiya na ƙaramar hukumar Kumbotso, wanda kuma shi ne ya wakilci Kantoman ƙaramar hukumar Alhaji Ɗan’iyala Inuwa ya bayyana wannan ƙungiya a matsayin zakaran gwajin dafi, musamman ganin ta fito da wani tsari wanda ake ganin ƙila nan gaba ita za a nemi ta tantance duk wani mai buƙatar takara. “Domin mun tabbata sai mai kishin ci gaban al’umma za su bai wa dama.” Inji shi

Kansilan ya bai wa masu hannu da shuni shawara da su bada tasu gudummawar wajen ci gaban wanann shiri. A ƙarshe ya tabbatar wa da mahalarta taron cewar zai isar da duk saƙon da ya karɓa a lokacin wannan taro.

Shi ma dagacin Ja’o’ji, Alhaji Sulaiman ya bayyana gamsuwa da shirye-shiryen wannan ƙungiya, saboda haka ya buƙaci gwamnatoci da yin duba da halin da al’umma suka tsinci kawunansu a ciki, musamman wannan annoba ta zazzaɓin cizon sauro. Ya ce, kamata ya yi ma gwamnati ta a je komai ta mayar da hankali don tunkarar wannan ibtila’i. Daga ƙarshe ya gode wa shugabannin wannan ƙungiya bisa wannan kyakkyawan tunani.

 

Exit mobile version