Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya amince da nadin Malam Fannami a matsayin shugaban ma’aikatan jihar Borno daga ranar 17 ga watan Yuli.
Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Malam Bukar Tijani ya raba wa manema labarai ranar Alhamis a Maiduguri.
- Sojoji Sun Yi Wa ‘Yan Fashin Daji Luguden Wuta, Sun Kashe 22 A Katsina
- Wasu Matasa Sun Kone Ofishin Jakadancin Sweden A Iraki Kan Kona Alkur’ani Mai Tsarki
Sanarwar ta kara da cewa an haifi Mallam Fannami a Damasak hedikwatar karamar hukumar Mobbar ta jihar Borno, a ranar 15 ga watan Junairu, 1966, kuma ya halarci makarantar firamare Damasak daga 1971 zuwa 1977 da kuma Government Technical Secondary School Buni Yadi daga 1977 zuwa 1982.
“Ya wuce Jami’ar Maiduguri a shekarar 1982 inda ya karanta fanni Shari’a, sannan ya sake karanta digirinsa na farko fannin shari’a a shekarar 1987, sannan ya wuce makarantar koyar da shari’a ta Nijeriya da ke Legas a shekarar 1987.
Ya yi hidimar kasa a ma’aikatar shari’a ta Jihar Neja, kuma ya kammala a shekarar 1989.
“Ya fara aikin gwamnati ne da ma’aikatar shari’a ta jihar Borno a matsayin lauyan jiha na II a ranar 29 ga watan Janairu, 1990 sannan ya zama sakataren ma’aikatar shari’a a ranar 16 ga Oktoba, 2009.
Daga nan kuma aka nada shi babban sakatare a ranar 27 ga watan Agusta, 2010.
“A lokacin da yake rike da mukamin babban sakatare, ya yi aiki a ma’aikatun gwamnati da dama kafin a nada shi a matsayin shugaban ma’aikata na rikon kwarya a ranar 21 ga Oktoba 2023.
“Barista Malam Fannami, memba ne a babbar Cibiyar Nazarin Siyasa da ke Kuru. Yana da aure da ‘ya’ya,” in ji sanarwar.