Gibin kasafin kudin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta samar a cikin shekara 8 na mulkinsa zai kai wani matakin da ba a taba samu ba na Naira Tiriliyan 55.3 in aka lura da kasafin kudin shekarar 2023 da aka sanya wa hannu na Naira Tiriliyan 21.83 wanda gibin kasafin ya kai Naira Tiriliyan 10 kamar yadda jaridar LEADERSHIP ta ruwaito.
Masana tattalin arziki sun bukaci gwanatin Nijeriya ta saurari gargadin Hukumar Lamuni ta Duniya (IMF) da Bankin Duniya a kan yawan bashin da ake bin Nijeriya musammman bashin da take karbar daga Babban Bankin Nijeriya wanda hakan yake kara haifar da hauhawar farashin kayan masarufi yana kuma karya darajar Naira da nakasa kudaden da ke asusun Nijeriya na kasashen waje.
Masana tattalin arzikin suna masu ra’ayin cewa, wannan halayyar ta cin bashi daga CBN yana nuna Nijeriya bata da kima da mutumcin cin bashi a cibiyoyin kudi na duniya ke nan, don cin bashi a CBN ba wani abu ba ne sai kawai a buga takardun kudi a watsa cikin harkokin tattalin arziki wannan babbar hatsari ne ga tattalin arzikin kasa.
Gibin Kasafin Kudi
Masana tattalin arzikinh sun nuna cewa, Nijeriya ta kure matakinta na cin bashi a kusan dukkan cibiyoyincin bashi na duniya, sakamakon haka kuma shi ne Nijeriya ba za ta iya yin cikakken hulda ta kudi ba a kasuwannin hada-hadar kudaden kasashen waje, hakan yake nuna da alamar tambayar cewa, wai a ina za a iya samun cike gibin fiye da Naira Tiriliyan 12 don tafiyar da kasafin kudin wannan shekarar na 2023.
Hanya daya tilo daya rage wa gwamnatin kuma ita ce ta yi watsi da akidarta na cin bashi ta kuma dora wa ‘yan Nijeriya haraji a kan harkokin kasuwancisu daban-daban don sajmar da kudaden da suka yi gibi a kasafin kudin.
Kididdigar da jaridar LEADERSHIP ta yi ya nuna cewa, dole duk dan Nijeriya ya biya akalla Naira 60,000 in har ana son a cika gibin Naira Tiriliyan 12 na kasafin kudin 2023.
Kuma a daidai lokacin da Shugaba Buhari zai bar karagar mulki wato ranar 29 ga watan Mayu na 2023, ofishin kula da basussuskan Nijeriya ya bayyana cewa, bashin da ake bin Nijeriya zai kai Naira Tiriliyan 77 wanda hakan ke nuna cewa, ana bin kowanne dan Nijeriya Naira 385,000 don biyan bashin da ake bin Nijeriya gaba daya.
Gwamnatin Buhari ta haifar da gibin da ya kai ga kashi -4.7 wanda shi ne ma fi kololuwa tun shekarar 1999 a lokacin yana kashi -5.4 kamar yadda kididdigar bayanai na tattaln arziki ya nuna.
A shekarar 2023, an samu babbar gibi a kasafin kudin da ba a taba samun irinsa ba a wannan gwamnatin tun da ta hau karagar mulki, kididdigar ya nuna cewa, an samu karin gibin da ya kai kashi 402.07 wanda ya ke nuna cewa, Naira Tiriliyan fiye da 12.1 maimakon Naira Tiriliyan 2.41 da aka samu a farrkon mulkin wannan gwamnatin, wanda ke nuna cewa, wannan ne mafi girma a cikin shekara 7.
A kasafin kudin shekarar 2016 wanda aka yi wa lakabi da “Budget of Change’, kasafin kudin da wannan gwamnatin ta fara cikakken aiwatarwa sai da gwamnatin ta ci bashin Naira Tiriliyan 2.41 don aiwatar da kasafin kudin da aka kiyasata ya kai Naira Tiriliyan 5.36.
Kasafin kudin 2023 kamar yadda Shugaba Buhari ya sanya wa hannun ya kai Naira Tiriliyan 21.83 an samu yi karin fiye da Naira Tiriliyan 1.32 a kan abin da bangaren gwamnati ta bayar na Naira Tiriliyan 20.51.
Ana sa ran samar da Naira Tiriliyan 9.73 don aiwatar da kasafin kudin, gwamnati ta kuma shirya tattaro Naira Tiriliyan 12.1 ta hanyar cin sabbin basuka daga kasashen waje da kudaden da sayar da wasu kaddarorin gwamnati zai samar.
A halin yanzu kuma Ministar kudi, Hajiya Zainab Ahmed ta bayyana cewa, gwamnati ba ta da shirin cin bashi daga cibiyoyin bayar da basuka na kasuwannin kasashen duniya.
A halin yanzu Nijeriya ta ci bashi daga Eurobond wanda ya kai Dala Biliyan 15 a kan haka Hajiya Zainab ta bayyana cewa gwamnati ba za ta nemi bashin Eurobond ba har sai an samu daidato a kasuwar shunku musamman ganin farashin Eurobond ya yi gaggarumin tashi a wannan shekarar a kasashen Afrika.
Zuwa yanzu Njeriya ta sayar da Eurobound har na Dala Biliy6an 1.25 a shekarar 2022 wanda ya kai ga Nijeriya a matsayin kasa ta 8 a cikin kasashe masu nauyin bashi a duniya, a kan haka Hajiya Zainab ta ce, Nijeriya za ta mayar da hankalinta ne a kan neman basuka daga Bankin Dunya da Bankin Musulunci da Bankin Bunkasa Afrika da sauran cibiyoyin bayar da lamuni na duniya don samun kudaden gudanar da kasafin kudin gaba daya.
Yanayin rashin armashin farashin Eurobond a kasuwanin Afirka musanmman matakin da kasar Ghana ta dauka a karshen shekara data gabata inda ta nemi masu binta bashi su yafe mata ruwan da ke tattare da basukan a daidai lokacin da kasar ke fama da dinbin bashin da ake abin.
A watan Yunin shekarar da ta gabata ana bin kasar Ghana Dala Biliyan 28.1 tana kuma biyan ruwan bashin daya kai har na kashi 68 na harajin da ake karba a daidai wannan lokacin.
A kan hakja shugaban kamfanin hada-hadar kudi a ‘Cowry Asset Management’, Mista Johnson Chukwu, ya ce Nijeriya ta kama hanyar shiga halin da kasar Ghana ta shiga in har ba a yi hankali ba. Tuni Nijeriya ta kashe kashi 100 a kudaden shigarta wajen biyar ruwan bashin da ake binta.
Ya kuma lura da cewa, zuwa yanzu wasu kasashe na bin Nijeriya kudade masu yawan gaske wanda hakan zai sanya Nijeriya ta ci gaba da biya makudan kudade wajen biyan basukan da ake binta ya hanyar cin bashi, ya kuma ce, da gibin kasafi a Naira Tiriliyan 12.1 ya zama dole kenan Nijeriya ta cigaba da cin bashi abin da kuma zai cigaba da kara yawan bashin da ake bin Nijeriya.
“A yau Ghana ta saba alkawarin biyan basukanta na cikin gida dana kasashen waje ya kuma yakamata Nijeriya ta yi taka tsantsan kada ta fada irin wancan tarkon. Duk wata kasa da ke cin bashi don ta biya bashi ta kama hanyar fadawa matsalar da zata halaka ta, kuma hanyar da Nijeriya ta ke bi kenan.
Shi kuwa Shugaban Kungiyar Masana Tattalin Arziki ta Kasa, Farfesa Godwin Owoh, ya nuna rashin amincewarsa ne a kan alkalummar da gwamnati ta fitar na kudaden da ta ce ta ci bashin su, musamman ba wata hukuma mai zaman kanta da ta tabbatar da wadannan alkalummar da aka ce an ci bashin su.
Farfesa Owoh ya kara da cewa, “Bayanan da suke fitowa daga IMF, Bankin Duniya da sauran kasashen duniya ya nuna cewa masu tafiyar da harkokin tattalin kasar nan sun gaza. Abin daya kamata kawai a gaggauta dakatarwa a halin yanzu shi ne cin bashi. Yaushe za a ce gwamnatin tarayya ta ci bashi daga Babban Bankin Nijeriya har na Tririyan 22 a kan ruwan Naira Tiriliyan 1?”
Ya shawarci wannan gwamatin miacid a ta dakatar da cin bashi hakan nan musamman ganin tunda ta kama hanyar kamamla wa’adin ta na mulki, ta yadda gwamnati mai kamawa za ta sake shirya wani sabon kasafin kudi don gudanar da ayyukanta, kuma gashi kasar Chana, IMF da sauran kasashe masu bayar da basukka sun fahimci ba zai yiwu su ci gaba da ba gwamnatin bashi ba.
Ya goyi bayan majalisar tarayya a kan yadda ta yi watsi da Naira Tiriliyan da aka ce an ci bashin su daga Babban Bankin Nijeriya (CBN), ta yaya za a karbi bayanin cewa, an karbi wadannan makudan kudaden a matsayin bashi kuma wai an biya bashi da su?.
Ya ce, hankali ma ba zai yarda da wannan ba, ta yaya masu zuba jari za su shigo?, bayan an riga an kashe dukkan kudaden. Wa gwamnati za ta biya kudaden? Wa yake da Babban Bankin, ai CBN wani bangare na fadar shugaban kasa ko kuma muna wata kasa ce daban?.” In ji shi.
A nasa jawabin, wani masanin tattalin arziki a yanjkin Afrika ta yamma, Farfesa Akpan Ekpo, ya nemi lallai gwamnati ta dakatar da yadda take cin bashi ba kan gado.’
Ya lura da cewa, babu wata illa a cin bashi musamman in za a gudanar da wasu ayyuyka ne masu muhimmanci da za su shafi rayuwar al’umma, ya kara da cewa matsalar da ke tattare da cin bashi a Nijeriya shi ne ana yi ne a boye, al’umma basu sanin abin da yasa ake ciwo bashin ba.
“Haka kuma kudaden da ake biyan ruwan bashi ya yi matuukar yawa. In aka lura da dukkan kasafn kudin da ake gabatarwa kusan kashi 10 a cikin dari ana amfani da shi ne don biyan ruwan basukan da aka ci, saboda haka dole mu yi takatsanstan.
“Ina tausayin gwamnati mai kamawa. Ga matsalolin bashin da aka ci ga kuma sauran matsaloli a gefe guda , za kuma a ci gaba da biyan wadanna basukan ne har al’umma masu zuwa, in har bamu yi hankali ba al’umma da za su zo a an gaba za su yita tsine wa kabarburan mu saboda basukan da muka dora musu don za su ga basuka su kuma kasa sanin abubuwan da aka yi dasu.
“Babu hanyoyi masu kyau, babu jiragen kasa masu kyau, babu ruwan sha mai kyau kuma gashi lamarin annobar korona ya tona asirn halin da bangaren kiwo lafiya yake ciki. Yanzu kusan fiye da shekara 20 kenan har yanzu muna biyan ruwan basukan da aka karba ba tare da an fara biyan ainihin basukan ba. Kuma gashi sai kara karbar bashin ake yi ba tare da wani lissafi ba.”