Tsoro Ke Hana APC Yin Babban Taron Kasa –Makarfi

192

Daga  Sulaiman Bala Idris, Abuja

Shugaban riko na jam’iyyar PDP, Sanata Ahmed Makarfi ya zargi jam’iyya mai mulki ta APC da cewa tsoro ne ke hana ta gudanar da babban taron jam’iyya na kasa. Ya ce, wannan shi ne dalilin da ya sa duk a tsawon shekarun da aka kwashe, jam’iyyar ta kasa shirya wannan taro mai dimbin muhimmanci.

Sanata Makarfi ya bayyana hakan ne jiya a Abuja a yayin da ya amshi shugaban kwamitin salo da dabarun habbaka fannin shari’a, Aminu Shagari, da wasu membobi a wata ziyarar sada zumunta da suka kai masa.

“Ana ta yi mana addu’ar gudanar da taron kasa cikin nasara. Alhamdu lillah, ba mu da wata fargaba saboda mu ba APC bane wadanda ke tsoron yin babban taron kasa.  Mu kuma ba mu jin wannan tsoron ne saboda muna bisa turbar dimokradiyya.” In ji shi

Cikin jawaban da Makarfi ya fadi wa bakin nasa, har da zantukan da suka shafi harkar shari’a, da irin matsalolin da ake fuskanta musamman ta fuskacin tsawaita shari’a.

Idan dai ba a manta ba, jam’iyyar PDP na shirye-shiryen gudanar da Babban Taronta na kasa a ranar Asabar mai zuwa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here