Ƙarin Kuɗin Siminti: Diloli Da Al’ummar Kano Sun Bayyana Rashin Jin Daɗinsu Ga Kamfanin BUA

‘Yan kasuwa masu sayar da siminti da al’umma masu saya sun nuna rashin jin daɗinsu da yadda Kamfanin Siminti na BUA ya ƙara farashi.

Rahotanni sun bayyana cewa, kamfanin na BUA ya yi ƙarin Naira 200 kan asalin kuɗin siminti buhu ɗaya, wanda a baya ana sayarwa da diloli kan kuɗi Naira 2,800 amma yanzu kamfanin ya ƙara farashi zuwa Naira 3,000.

Dilolin siminti da sauran jama’a sun shiga fargaba ne bisa tunanin cewa matuƙar aka ƙara wa diloli naira 200, hakan na nufin a baya suna sayar da simintin Naira 3,600 amma yanzu zai koma Naira 3,800 a kasuwa.

Binciken wani bincike da majiyarmu ta gudanar a Kano yau Laraba ya tabbatar da cewa, diloli da masu sayen siminta sun shiga cikin matsanancin zulumi bisa ƙarin farashin.

Wani mai kasuwancin sayar da siminti a Kano kuma mai kamfanin buga bulo na Sallari Blocks, Musa Shehu ya ce sun samu labarin ƙarin farashin da kamfanin ya yi wa diloli, amma abin bai sakko zuwa gare su ba tukunna.

Shehu ya ce: “Har zuwa yanzu dai muna sayar da buhu kan kuɗi Naira 3,550 zuwa 3,600 amma babu makawa nan ba da jimawa ba ƙarin kuɗin zai iso mana.

“Samun ƙarin farashin simintin na BUA tabbas zai wahalar da al’umma, musamman bisa la’akari da halin ƙunci da ake fama da shi a faɗin ƙasar.

“Muna kira ga kamfanin BUA da su taimaka su janye wannan ƙarin farashi domin babu makawa zai shafe mu, kuma zai tilasta mutane su daina sayen siminti daga wurinmu.” Inji shi

Shi ma Auwalu Umar wani mai sana’ar sayar da siminti ya bayyana cewa, a al’ada farashin siminti ya kan sakko a lokacin ruwa, musamman ma a Arewacin Nijeriya, wannan ne ya sa ya cika da mamaki bisa ƙarin farashi daga kamfanin BUA.

Ya ce: “Wannan tabbaci muke da shi, na rantse cewa, matuƙar wannan ƙarin farashin ya tabbata toh mutane za su daina sayen siminti daga wurinmu, idan kuma haka ya faru, mu ne da asara, ba kamfanin BUA ba.”

Wasu dilolin kamfanin siminti na BUA a Kano, waɗanda suka nemi a sakaya sunansu sun yi Allah wadai da wannan ƙarin farashi, sun kuma koka da irin halin da wannan mataki zai jefa mutane.

Dilolin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sa baki cikin wannan lamari don a samu mafita.

 

Exit mobile version