Daga Abubakar Abba, Kaduna
Shugaban ƙungiyar ‘yan Jarida masu yaƙi da cutar shan Inna reshen
Jahar Kaduna (JAP), Alhaji Lawa Dogara ya sanar da cewa, za a fara gudanar da allurar cutar ranar 14 zuwa 19 ga watan Okutobar shekarar 2017.
A sanarwar da Alhaji Dogara ya sanywa hannu ya kuma baiwa Jaridar LEADERSHIP A Yau, ya ce, za a gudanar da allurer a gida- gida da kasuwanni da tashar mota da kan manyan hanyoyi.
Ya yi kira ga iyaye da waɗanda yara ke ƙarƙashin su, dasu bada haɗin kai don cin nasarar shirin, musamman don baiwa masu gudanar da allurer goyon baya.
Shugaban ya roƙi sarakuna da malaman addini da kada su gajiya wajen goyon bayan da suke badawa an yaƙar cutar.