Rundunar Ƴansandan ta ƙasa reshen jihar Gombe ƙarƙashin jagoranci CP Hayatu Usman psc ta samu nasarar kama masu satar ƙarfen hanyar jirgin ƙasa wato (Railway Track Sleepers)
Hukumar ta samu nasarar damke mutane huɗu ne da ake zargi da cirewa tare da satar ƙarfen tarogon jirgin ƙasa a ranar 29/05/2024 da misalin ƙarfe 8:40pm, bayan samun bayanan sirri daga mutanen gari.
- Gwamna Inuwa Ya Ƙaddamar Da Sabon Kamfanin Taki A Gombe
- Liƙi Da Takardun Naira Ya Jefa Wata Mata Komar EFCC A Gombe
Waɗanda ake zargin sun haɗar da:
Ibrahim Yauta mai shekaru 30 da ke Unguwar Uban Doma Liji Yelmantu da Kasimu Umar mai shekaru 26 mazaunin Bogo garin – Waziri bye-pass, sai kuma Yusuf Mohammed mai shekaru 32 da ke Kofar Sarkin Liji, da kuma Shu’aibu Saidu Unguwa Uku, Gombe.
Matasan an kama su ne ɗauke da ƙarafunan hanyar jirgin ƙasa guda 42 a cikin motar ɗibar yashi/bulo a inda bayan tuhumarsu suka amsa laifinsu tare da bayyana sunan waɗanda suke sayarwa idan sun sato mai suna Shu’aibu Saidu mazaunin Unguwa Uku, Gombe.
Kakakin rundunar ASP Buhari Abdullahi, ya ce, masu laifin ya tabbatarwa da hukumar Ƴansanda cewar wannan shi ne karo na bakwai da yake satar ƙarfen jirgin kuma yana sayar da shi a kan farashi kamar haka; Naira dubu biyu ₦2000, dubu uku ₦3000 a wannan karin kuma sun yi da mai siyan ƙarfen a kan Naira dubu huɗu ₦4000.