Wata ‘yar majalisar dokoki a Jamhuriyar Nijar, ta yi kira ga ‘yan uwanta ‘yan majalisa maza da mata da su kafa wata dokar da za ta warware sarkakiyar da ke kunshe cikin dokokin kasar game da matsayin ‘yan luwadi da madigo.
BBC Hausa ta rawaito cewa, wannan na zuwa ne bayan da a makon jiya aka gurfanar da wasu mata da ake zargi da aikata madigo a gaban kotu, inda mai shari’ar ya kasa samun wata madogara daga dokokin kasar da zai iya amfani da ita wajen yanke musu hukunci.
- Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane Fiye Da 130 Cikin Wata Biyu A Nijar
- Jakadan Kasar Sin Dake Nijar Ya Gana Da Tsohon Shugaban kasar
‘Yar majalisar, Honorable Nana Djoubie Harouna Mati, ta shaida wa BBC cewa ‘yan kasar ne suka fito suka nemi majalisar da ta kafa doka da za ta haramta ayyukan ‘yan luwadi da madigo.
‘Yar majalisar ta ce bukatar hakan ya taso ne saboda a baya-bayan nan ne wani bidiyo ya nuna wasu ‘yan mata na yin madigo tsakaninsu wanda kuma ya zama tilas hukumomi su dauki mataki nan take.
Honorabul Nana Djoubie ta kuma ce babu wata doka a kasar ta hukunta mutum idan aka same shi da laifin yin madigo ko luwadi, adon haka haka ne suka tashi haikan wajen ganin sun kafa doka da ta kamata domin takawa lamarin burki tun bai ta’azzara ba.