ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ɗalibai Sun Rubuta Jarrabawar WAEC Cikin Dare A Duhu

by Abubakar Sulaiman
7 months ago
WAEC

Wasu ɗaliban sakandare a sassa daban-daban na Nijeriya sun rubuta jarrabawar harshen Ingilishi ta WAEC (West African Senior School Certificate Examination) a duhu da daddare a ranar Laraba, sakamakon rashin wutar lantarki da matsalolin tsaro da suka hana gudanar da jarrabawar cikin kwanciyar hankali.

Rahotanni daga shaidu da kuma bidiyo da hotuna da suka karaɗe kafafen sada zumunta sun nuna cewa jarrabawar, wadda ke ɗaya daga cikin muhimman takardu ga ɗalibai, an gudanar da ita har zuwa ƙarfe 9:45 na dare a wasu cibiyoyi. Ɗalibai sun yi amfani da fitilar hannu, da lanpo, da fitilar wayarsu wajen kammala jarrabawar a jihohin Delta, Oyo, Benue, Osun da Ogun.

  • Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (2)
  • Abin  Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (1)

Wani mai amfani da dandalin X, mai suna @omolomo, ya wallafa bidiyo da hotunan da suka nuna dalibai na rubuta jarrabawa a cikin duhu.

ADVERTISEMENT

“Wannan wata makaranta ce a Nijeriya cibiyar rubuta jarrabawar WAEC. Yanzu haka suna rubuta jarrabawa cikin duhu, da fitilun hannu da lanpo. Wannan hoton yana nuna gaskiya, ba karya ba,” inji shi.

WAEC WAEC

Wasu rahotanni na nuna cewa jarrabawar da aka tsara a yi da rana, ta fara a wasu makarantu tsakanin ƙarfe 4:00 na yamma zuwa 7:00 na dare, inda aka kammala a wasu wurare kusan ƙarfe 9:00 ko ma fiye da haka. Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun ce jinkirin ya faru ne sakamakon zargin fitowar satar amsar jarrabawar kafin lokacin rubutawa.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3

Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148

Daga baya, hukumar WAEC ta fitar da sanarwa tana mai bada hakuri, inda ta ce wasu ƙalubale ne suka hana isar da kayayyakin jarrabawa akan lokaci. Wannan lamari ba sabon abu ba ne, domin a watan Afrilu, LEADERSHIP ta ruwaito cewa wasu masu rubuta jarrabawar UTME sun bar gida da asuba domin isa cibiyoyin jarrabawa kafin ƙarfe 6:30 na safe, ba tare da wadataccen tsaro ko sufuri ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3
Ilimi

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3

December 14, 2025
Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148
Ilimi

Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148

December 14, 2025
Fadar Shugaban Kasa Ta Karrama Daliban Da Suka Nuna Hazaka A 2025
Ilimi

Fadar Shugaban Kasa Ta Karrama Daliban Da Suka Nuna Hazaka A 2025

November 30, 2025
Next Post
Atiku Ya Caccaki Gwamnatin Tinubu, Ya Yi Gargaɗi Kan Cin Sabon Bashi

Atiku Ya Caccaki Gwamnatin Tinubu, Ya Yi Gargaɗi Kan Cin Sabon Bashi

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.