Connect with us

NOMA

Published

on

An Shawarci Manoma Su Tuntubi Hukumar GSADP Kafin Sayen Maganin Kashe Kwari

 

An yi kira ga maoman dake jihar Gombe dasu dinga tuntubar don samun shawarwari kafin su sayi magungunna kashe kwari a kasuwanni don gudun kada su sayen amfanin gona mai dauke da guba.

Kiran ya fito ne daga bakin Manajan shirn aikin noma na GSADP na jihar Gombe Mista Binus Maina.

Manajan shirn Mista Binus Maina wanda ya sanar da hakan a hirarsa da mamema labarai jihar Gombe ya ce, Yace, yana son maoman su sani cewar, duk yadda suka shiya don yin noma idan har basu samu ingantaccen irin noma ba, faha baza su samu yin girbi mai kyau ba.

Ya kuma sanar da cewa, shirin, zai noma kadada 365 ta irin gona a daukacin kananan hukumomi sha daya dake cikin jihar.

Manajan shirn Mista Binus Maina ne ya sanar da hakan a jihar ta, inda ya yi nuni da cewar, manufar ita ce don a samar da ingantaccen irin gona ga maoman jihar ta Gombe.

A cewar Manajan Mista Binus Maina, baya ga irin noman da kamfanonin dake jihar suke samarwa, zamu kuma zamu kuma samar da gona don a rubanya irin, musamman don magance bara gurbin da suke sayar da irin noman na jabu a kasuwanni.

Manajan shirn Mista Binus Maina yaci gaba da cewa, shirin zai taimaka matuka wajen samar da ingantaccen irin noma don rabarwa da monama.

A wata sabuwa kuwa, Kananan manoma dake a kannan hukumomi dake a cikin jihar, jihar Borno zasu sanu tallafin yin noma daga gin gwamnatin tarayya.

Kananan hukumomin sun hada da, Maiduguri, Jere, Bama, Konduga, Gwoza, Biu, Chibok, Askira Uba, Monguno, Magumari, Nganzai da kuma Mobbar.

Malam Basharu Ibrahim wani jami’I a Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, ya sanar da hakan a Maiduguri, inda ya ce, manoma guda 12,000 zasu amfana d tallafin.

Ya ce, gwambatin ta yi kudurin yin hakan ne ganin yadda yakin yan kungiyar Boko Haram ya daidaita jihar Borno.

Jami’in shirin na Hukumar ta bayar da agajin ta kasa Malam Basharu Ibrahim ya ci gaba da cewa, ya zuwa yanzu Hukumar tayiwa manoma guda 12,000 rijista da yakin na yayan kungiyar Boko Haram ya daidaita don suma su amfana da shirin.

A cewar Malam Basharu Ibrahim, Gwamnatin Tarayya ta wanzar da shirin ta karkashin Cibiyar wadata kasa da abinci na NFSC, har ila yau, an kuma tsara shirin yadda manoman zasu iya samun takin zamani da sauran kayan ainin noma.

Ibrahim ya cigaba da cewa, shirin zai kuma mayar da hankali wajen tattaro manoman da abin ya shafi don shiga yin shula da kuma koyon kiwo.

A cewar jami’in Malam Basharu Ibrahim Hukumar zata kuma rabar da Irin noma da kayan feshi ga manoman don suma suyo shuga a daminar shekarar 2019.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: